An wayi gari da firgici a garin Minna, babban birnin jihar Neja, lokacin da wani da ake zargin dan kungiyar Boko Haram ne ya yi artabu da jami’an tsaro a daren Talata.
Jami’an tsaro ne suka kai samame a Unguwar Gebganu da ke Minna, inda gidan wanda ake zargin yake.
- Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Kujerar Gwamnan Adamawa A 28 Ga Oktoba
- Gwamnan Zamfara Zai Binciki Badakalar Miliyan 774 A Hukumar Alhazai Ta Jihar
Daily Trust ta rahoto cewa, an gano a kalla bindigu kirar AK47 guda 150, harsashai kusan 3,000, bama-bamai, makamin roka da kuma bindigar harbo jirgin yaki a gidan wanda ake zargin.
Mazauna yankin sun ce, an kwashe sa’o’i da dama ana artabu da jami’an tsaro da wanda ake zargin wanda aka fara da misalin karfe 12 na dare kafin daga bisani ya tsare ta bayan gida.
An rahoto cewa, ya yi amfani da makamin roka ne ya rushe wani bangare na katangar gidansa inda ya fita ya tsere, amma jami’an tsaro sun kama matarsa da ‘ya’yansa.
An bayyana cewa wanda ake zargin ya fara harbe-harbe ne a lokacin da ya lura da isowar jami’an tsaron ta kyamarar CCTV da ya makala a gidansa.