Ofishin jakadancin Sin dake kasar Zimbabwe ya bayyana cewa, cinikayya tsakanin Sin da Zimbabwe a cikin watanni 9 na farkon bana, ya karu da kashi 39.4 cikin 100, zuwa dalar Amurka biliyan 2.43, idan aka kwatanta da makamancin lokaci a shekarar da ta gabata, wanda ya zarce jimillar cinikin da aka yi a shekarar 2022.
A cewar ofishin jakadancin, darajar kayayyakin da Zimbabwe ta fitar zuwa kasar Sin a cikin wannan lokaci, ta kai dalar Amurka biliyan 1.36, yayin da darajar kayayyakin da aka shigo da su cikin kasar daga kasar Sin, ta kai dalar Amurka biliyan 1.07. Yana mai cewa, kayayyakin da kasar Sin ta ci gaba da shigo da su cikin kasar, sun taimakawa Zimbabwe wajen samun rarar cinikayyar da ta kai dalar Amurka miliyan 29.
- Xi Jinping Ya Gana Da Gwamnan Jihar California Dake Amurka
- Me Ya Sa Dangantaka Da Sin Ke Samun Karbuwa A Afrika?
A cewar hukumar kididdiga ta kasar Zimbabwe, a cikin watan Agusta, kasar Sin ta kasance kasa ta uku wajen fitar da kayayyaki zuwa kasar Zimbabwe, inda makwabciyarta Afrika ta Kudu ta kasance a kan gaba, sai hadaddiyar daular Larabawa a matsayin babbar kasuwa ta biyu a fannin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje. Dangane da shigo da kayayyaki kuwa, a watan Agusta, kasar Sin ta kasance babbar kasuwa ta biyu ga Zimbabwe, bayan Afirka ta Kudu.
Sannan a yau Laraba 25 ga watan Oktoba, ranar yaki da kakaba takunkumi ce da kungiyar raya kudancin Afirka ko kuma SADC a takaice ta ayyana. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, kasarta ta sake kira ga wasu kasashe da kungiyoyi ’yan kalilan, da su saurari muryoyin kasashe daban-daban, da gaggauta soke takunkuman da suka kakabawa kasar Zimbabwe ba bisa doka ba, da daukar matakai a zahirance, don taimaka mata habaka tattalin arziki da kyautata rayuwar al’umma, gami da taka rawar gani a fannin shimfida zaman lafiya da samar da ci gaba a duniya baki daya.
Mao ta jaddada cewa, Sin za ta ci gaba da goyawa Zimbabwe baya wajen nuna adawa ga shisshigin da wasu kasashe suka yi mata, don ta kama tafarkin samar da ci gaba bisa ’yancin kanta. (Ibrahim Yaya, Murtala Zhang)