Kotun sauraren kararrakin zaben ‘yan majalisar tarayya ta tabbatar da zaben tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal a matsayin halastaccen zababben dan majalisar dattawa mai wakiltar Kudancin Sakkwato.
Alkalai uku a karkashin jagorancin mai shari’a Denis Echesi a zamansu na yau sun yi watsi da karar da jam’iyyar APC da dan takararta, Sanata Ibrahim Danbaba suka shigar suna kalubalantar nasarar PDP da dan takararta.
- Sin Ta Gabatar Da ’Yan Sama Jannatin Da Za a Harba A Kumbon Shenzhou-17
- Pedri Ba Zai Buga El-Clasico Ba Saboda Rauni
Kotun a Sakkwato ta bayyana cewar masu karar sun kasa gabatar da gamsassun hujjojin karar da suke yi.
A kan hakan kotun ta ci su tarar dubu 200.
Lauyan Tambuwal, Sulaiman Usman (SAN) a tattaunawarsa da manema labarai ya bayyana hukuncin a matsayin na adalci.
Ya ce kotun ta yi watsi da karar ne saboda hujjojin da suka gabatar ba amintattu ba ne.
A nasu bangaren kuma sun gamsar da kotu cewar zaben Tambuwal halastacce ne wanda aka gudanar daidai da dokokin zabe.
Daya daga cikin lauyoyin da suka wakilci Sanata Danbaba, Chris Kelechi ya bayyana cewar za su yi nazarin hukuncin kotun domin daukaka kara.