Sakamakon barin wuta da fatattakar da kasar Isra’ila ke yi a yankin Gaza, Jakadan Falasdin a Nijeriya, Abdullah Abu Shawesh ya yi kira ga dukkan duniya ta yi musu adalci a kan barnar da Isra’ila ke aikatawa a yankinsu.
Ya bayyana cewa kisan kiyashin da ake wa Falasdinawa ya kai matsayin inna-naha, saboda a kullu yaumin ana kashe fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba ciki har da dubban mata da yara tun daga ranar 7 ga Oktobar nan da Isra’la ta fara kai hare-hare a Gaza.
- Gobe Za A Tsame Duk Ma’aikacin Tarayya Da Ba Ya Cikin Tsarin IPPIS Daga Biyan Albashi
- Sabon Tsarin Biyan Albashi: Gwamnati Za Ta Cire Ma’aikatan Da Ba A Tantance Su Ba, Gobe
Abu Shawesh wanda ya kira taron manema labarai na musamman a ofishin jakadancin Falasdin da ke Abuja, ya ci gaba da bayanin cewa, “Sojojin Mamaya na Isra’ila sun kaddamar da mummunan yaki a kan Falasdinawa a yankin Falasdin da aka mamaye musu ciki har da gabashin Urshalima. Daga lokacin da suka kaddamar da yakin, suna ci gaba da kisan kiyashi a yankin. Daga ranar 7 ga Oktoba zuwa farkon makon nan, Falasdinawa sama da 6,000 fiye da rabi mata da yara sun yi shahada, kana sama da 1,800 sun ji munanan raunuka.
“Sannan an kashe jami’an kiwon lafiya 68, yayin da aka ji wa sama da 100 raunuka. Motocin daukar marasa lafiya 25 sun daina aiki. Isra’ila tana amfani da makami mai zagwanye fatar jikin Dan’adam wadda babu maganinsa a Gaza saboda yana bukatar tiyata ta musamman.
“Ana wa masu raunuka tiyata ba tare da an yi musu allurar kashe zafin ciwo ba ta hanyar amfani da hasken waya. Manyan Asibitoci 12 da cibiyoyin kiwon lafiya 32 duk ba su aiki saboda hare-haren Isra’ila da rashin man inji.”
“Mutanen da suka tsere suka bar muhallinsu ‘yan asalin yankin Gaza sun haura sama da miliyan daya da dubu dari hudu, sannan wadanda suka tsere tare da wasu iyalan da ba nasu ba sun kai 685,000, kana akwai 565,000 da suka tsere zuwa makarantu 148 da ke karkashin Hukumar Ba Da Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, haka nan akwai wasu 101,000 da suke masallatai da coci-coci da sauran wurare na jama’a, baya ga 70,000 da suke wasu makarantu na daban guda 67, kuma har yanzu wannan adadi yana ci gaba da karuwa.”
Har ila yau, Abu Shuwesh ya ce hare-haren na Isra’ila sun lalata gidaje sama da 181,000 ciki har da guda 20,000 da aka ruguza su gaba daya.
Abubuwan da Isra’ila ke aikatawa ba su tsaya nan ba, a cewar Jakadan, “A Gabar Yammacin Kogin Jordan, sojojin mamayar Isra’ila sun yi kisan gilla ga Falasdinawa 91 daga ranar 7 ga Oktoba zuwa farkon makon nan, kuma galibinsu kananan yara ne. Haka nan an tsare Falasdinawa 6,500 a cikin shekarar nan kawai, ciki har da guda 1,215 da aka kama daga 7 ga watan nan.
“Akwai Omar Daraghmeh mai shekara 58 da aka tsare a ranar 8 ga Oktoba da Arafat Yasser Hamdan dan shekara 25 da haihuwa wanda aka tsare a ranar 22 ga Oktoba, duka an kashe su ta hanyar azabtarwa a gidajen yarin Isra’ila.” In ji shi.
Jakadan ya kuma bayyana cewa yanzu haka minista Itamar Ben Giber mai tsananin akidar yahudanci ya fara raba wa Yahudawa ‘yan share wuri zauna a Gabar Yammacin Kogin Jordan makamai, kuma hakan zai kara yawan ta’asar da ake wa Falasdinawa a nan.
Hakazalika, Abu Shuwesh ya ce suna tir da gangamin bata-sunan Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutterers da shugabannin Isra’ila da kawayenta na Turawan Yamma suka kaddamar, saboda kawai yana tsage gaskiya a kan asalin abubuwan da ke faruwa a Gaza.
A cewarsa, wannan wata boyayyiwar manufa ce ta rufe bakin mutane da barazana ga duk wanda yake sukar ta’addancin da Isra’ila ke yi tare da neman a yi aiki da dokokin kiyaye rayukan bil’adama na duniya.
Dangane da goyon bayan da Turawan Yamma ke wa Isra’ila kuwa, Jakadan na Falasdin a Nijeriya, ya ce “yana da matukar ban takaici irin yadda shugabannin Turawan Yamma masu goyon bayan Isra’ila ke tururuwar bayar da cikakkiyar gudunmawar makamai da huldar siyasa a kan kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a Gaza, da fadar kalamai na rashin adalci ga Falasdinawa, inda hakan ya sake bai wa Isra’ila damar ci gaba da kisa, tabbas wannan zai kara yawan kisan da ake wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, da ruguza gidajen Falasdinawa da ababen more rayuwa tare da kara jefa rayuwar Falasdinawa cikin kunci musamman mata da yara.”
Jakadan ya yi kira ga manema labarai su cire son zuciya su rika bayar da rahotannin asalin abubuwan da suke faruwa, kana ya bayyana takaicinsa a kan yadda kafafen yada labarai na Turawan Yamma suka rungumi yada farfagandar Isra’ila ba-ji-ba-gani.
Da aka tambaye shi ko me kasashen Larabawa ke yi wajen kawo wa Falasdin dauki? Jakadan y ace, “Kasashen Larabawa har ma da na sauran musulmi a duniya da ma sauran masu tausayin dan’adam suna iya bakin kokarinsu. Amma kuma babu wanda zai iya zuwa Falasdinu kai-tsaye ba tare da ya bi ta yankin da Isra’ila ta mamaye ba. Muna jinjina wa wadanda suke tir da kwararar da jinin fararen hula da ta’asar da Isra’ila ke tafkawa. Su shugabannin Yamma kamar Joe Biden na Amurka abin kunya ne a ji su suna fadar kalamai na karaikarayin da Netanyahu ya tsegunta musu. Sun hau turbar karaikarayi suna juya wa gaskiya baya, wannan babban abin bakin ciki ne.” Ya bayyana.
Bugu da kari da aka tambaye shi, katamaime me za a yi a magance wannan matsalar, Jakada Abu Shuwesh ya bayyana cewa, “a bi dokokin da duniya ta yarda da su. A yi aiki da da daftarin Majalisar Dinkin Duniya. Muna sake jaddadawa, a bi dokokin kasashen duniya ba tare da zaben sashen da aka ga dama kuma a yi watsi da wani ba.”
Daga bisani, Jakada Abu Shuwesh ya nanata cewa, Falasdinawa suna da cikakken ‘yancin zaba wa kansu makoma da diyauci da kare hakkinsu na ‘yan adam wanda Isra’ila da Turawan Yamma kawayenta suke dannewa baki daya.
Kana ya yi gargadin cewa matukar kasashen duniya ba su tashi tsaye wajen kiyaye aiki da dokokin da duniya ta amince da su ba, munafurcin da ake yi zai ci kasashen har a cikin gidansu.