Mazauna Kauyen Kuyello a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, sun nuna damuwarsu kan bayyanar ‘yan ta’addar Ansaru a yankunansu.
An ruwaito cewa, ziyarar bazata a ‘yan kwanan baya da ‘yan Ansarun suka kai a kan baburansu a yankunan, ta jefa fargaba a zukatan mazauna yankunan wanda ke cikin Karamar Hukumar Birnin Gwari.
- CMG Ta Gabatar Da bukukuwan Baje Kolin Al’adun Sin Na Musamman A “Palace of Nations” Da Kasar Masar
- Kuskure Ne A Ɗauka RARARA Ba Kowan Komi Ba Ne – Farfesa Malumfashi
Kazalika, an ruwaito cewa, wasu daga cikin mazauna yankunan sun gargadi ‘yan kungiyar ta Ansaru da su fice daga yankunansu.
Bugu da kari, rahotannin sun ce, “‘yan Ansaru na gudanar da ayyukansu a kauyukan Kazage, Unguwar Gwandu, Unguwar Gajere, da kuma tsohon garin Kuyello, inda suke jan ra’ayin matasa suna shiga cikin kungiyar ta Ansaru domin su kara yawan adadin ‘ya’yan kungiyar a karamar hukumar. ”
Wani babba daga cikin mazauna kauyen, Malam Muhammadu Kuyello, ya tabbatar da cewa, ‘yan Ansaru sun shiga cikin Kuyallo ta hanyar garin Dan Auta, inda suka wuce, ba tare da sun ce wa kowa uffan ba.
Kazlika, ya sanar da cewa a yanzu haka, Ansaru sun dauki kimanin matasa 50 na tsohon garin Kuyallo a cikin kungiyarsu, inda kuma suka aurar da ‘yan mata bakwai.
A cewarsa, idan gwamantin jihar ta tura jami’an tsaro zuwa tsohon garin Kuyello, ‘yan kungiyar ba su da wani zabi illa su arce daga garin.
Bugu da kari, wani jagoran matasa a yankin Baban Yara Isa, ya ce, idan har mahukunta ba su kawo dauki ba, mazauna yankin za su yi artabu da ‘yan kungiyar da nufin fatattaksrsu daga yankin.
Ya ce, tuni masu fada aji a yankin suka sanar da mahukunta daban-daban da ke karamar hukumar akan lamarin, inda ya yi kira ga mahukuntan da su gaggauta daukar mataki.
Shi ma shugaban ci gaban masarautar Birnin Gwari (BEPU) Ishak Kasai, ya tabbatar da lamarin.
Sai dai, kakakin rundunar ‘yansanda na Jihar Kaduna ASP Mansir Hassan ya ce, bai da hurumin yin magana akan lamarin.