Babban jami’in diflomasiyyar kasar Sin ya bayyana a jiya Juma’a cewa, yana ziyara a kasar Amurka domin tattaunawa da bangaren Amurka kan aiwatar da muhimman matsaya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, ta yadda za a tabbatar da daidaito da hana zaman lafiya tsakanin Sin da Amurka daga tabarbarewa, da dawo da alakarsu kan ingantaccen tafarkin ci gaba nan ba da jimawa ba.
Wang Yi, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar ya bayyana hakan ne yayin ganawa da shugaban kasar Amurka Joe Biden a birnin Washington D.C.
- Bayan Nasara A Kotun Ƙoli, Tinubu Zai Ci Gaba Da Aikin Gina Nagartacciyar Ƙasa – Minista
- CMG Ta Gabatar Da bukukuwan Baje Kolin Al’adun Sin Na Musamman A “Palace of Nations” Da Kasar Masar
Ya shaida wa Biden cewa manufar kasar Sin daya tilo a duniya da sanarwoyin hadin gwiwa guda uku tsakanin Sin da Amurka, su ne ginshikai mafi muhimmanci na dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, wadanda dole ne a kiyaye su ba tare da tsangwama ba.
Wang ya ce, “Ya kamata mu mutunta ka’idoji guda uku na mutunta juna, da zaman lafiya da samun moriyar juna da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar don daidaita dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.” Ya kara da cewa hakan ba wai kawai ya dace da muhimman muradun kasashen biyu da al’ummomin kasashen biyu ba ne, har ma da fatan al’ummar duniya baki daya.
Biden ya yi karin haske kan matsayinsa na dora muhimmanci kan dangantakar dake tsakanin Amurka da kasar Sin. Ya ce, Amurka a shirye take ta ci gaba da tuntubar kasar Sin, tare da tinkarar kalubalen duniya baki daya.
Shi Ministan harkokin wajen kasar Sin dai, yana ziyarar kwanaki uku a Amurka daga ranar 26 ga wata.
A lokacin da yake tattaunawa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, Wang Yi ya kuma yi kira da a samar da “Abubuwa biyar da suka zama dole” a dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Ya ce dole ne bangarorin biyu su kiyaye fahimtar juna da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da daidaita huldar dake tsakanin kasashen biyu, da barin hanyoyin sadarwa a bude, da daidaita bambance-bambance tsakanin kasashen biyu da sabani yadda ya kamata, kuma dole ne a inganta hadin gwiwar moriyar juna.
Wang Yi ya kuma gana da mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Amurka, Jake Sullivan, inda ya jaddada cewa, babban kalubale ga dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka shi ne “Yancin kai na Taiwan” .(Yahaya)