Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa ta tabbatar da zaben Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin zababben gwamnan jihar a zaben gwamnan da aka yi aranar 18 ga watan Maris, 2023.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa bayan zaben gwamnan jihar Adamawa, wanda ya kai ga sake kada kuri’a wanda ya jawo cece-kuce, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana gwamna Fintiri mai ci, wanda ya nemi tazarce a matsayin wanda ya lashe zaben.
A zaben da aka sake gudanarwa a watan Afrilu, Fintiri na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 430,861, inda ya doke Aisha ‘Binani’ Dahiru ta jam’iyyar APC wadda ta samu kuri’u 398,738.
Binani da wasu ’yan takara sun kai karar kotu suna neman a soke nasarar Fintiri, amma kotun a ranar Asabar ta tabbatar da nasarar gwamna mai ci a karo na biyu.
Idan za a tuna Kwamishinan Zabe na Jihar (REC), Hudu Yunusa-Ari, ya bar baya da kura bayan kammala zaben da aka yi a ranar 15 ga Afrilu, 2023, lokacin da ya bayyana ‘Binani’ a matsayin wacce ta lashe zaben.
Lamarin da ya sanya INEC ta soke hukuncin Yunusa-Ari tare da dakatar da shi yayin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Daga nan ne INEC ta kammala zaben kuma ta sanar da Fintiri a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka sake gudanarwa.