Babban sakataren kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS) Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin samar da kyakkyawar fahimtar al’ummantaka ga jama’ar kasar Sin, don sa kaimi ga ingantacciyar bunkasuwar ayyukan jam’iyyar kan harkokin kabilu a sabon zamani. .
Xi ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a lokacin da yake jagorantar taron nazari na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS.
Xi ya kara da cewa, ya kamata a yi kokarin wayar da kan jama’a cewa mutane daga kowace kabila suna cikin al’umma daya ne, kuma makomarsu daya ce, kuma duk rintsi duk wuya babu rabuwa da juna. (Yahaya)