Kamar kowanne mako wannan shafi ya kan zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; Zamantakewar Aure, Rayuwar Yau da Kullum, Rayuwar Matasa, Soyayya da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin mazan da suke nuna halin ko inkula a kan yaransu, sai dai su sakar wa iyaye mata nauyin komai, har a rinka yi wa yaran kallon su ‘ya’yan mace ne. Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu, inda suka bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:
Sunana Rashida Abdullahi Salis Bungudu (Princess Bungudu)
Haka ne, da yawa wasu mazan ba sa iya tsinanawa yaransu komai sai dai su barsu da iyaye Mata, dalilin da ya sa mazan suke yin haka kuwa shi ne; wasu sabida talauci, wasu kuma san zuciya ke kawo hakan. Matsalolin da zai iya afkuwa; zai iya saka wani dar a zuciyar yaran zuwa ga iyayensu maza, su kasance ba sa ganin girmansu da darajar su. Idan ka yi wa yaran magana ‘me ya sa?’ za su ce ‘sabida babansu bai san damuwarsu da dawainiyar su ba’. Hanyar da za a magance irin hakan shi ne; ta hanyar kau da zaman banza, ya kasance kowa na da sana’ar yi, to in sha Allah za a kau da wannan matsalar. Iyayenmu su sani mu dinnan amanar Allah ce a gurinsu, su tsaya su ba mu tarbiyya daidai iya warsu watarana za su ci moriyyar mu da yardar Allah.
Sunana Aminu Adamu Malam Madori Jihar Jigawa:
Tabbas wannan al’amari yana faruwa kuma hakan yana jawo tabarbarewar tarbiyya, domin uwa ita kadai ba za ta iya bada cikakkiyar tarbiyya ba, tarbiyyar yara abu ne dake bukatar kulawar da ta dace. To magana ta gaskiya sakaci ne yake sa maza suke barin ragamar tarbiyya a hannun iyaye mata, domin kowa da nashi bangaren wajen gudanar da tarbiyyar yara, don haka duk wanda bai kula da nashin bangaren ba to dole tarbiyya ta samu tasgaro. To hakika malaman addinin musulunci ya kamata su maida hankali wajen yi wa Al’umma tunatarwa akan muhimmancin bada tarbiyya ga iyaye a musulunci da kuma matsin Uba da uwa a fannin tarbiyya a musulunci haka ne zai taimaka wajen magance wannan matsala. To shawarar da zaa ba su ita ce su ji tsoron Allah, domin ‘ya’ya kiwo aka basu kuma za a tambaye su akan yadda suka kula da tarbiyyar su, don haka ya kamata mutum yayi iya iyawar sa ya kuma dage da addu’a sai Allah ya yi riko da hannayensa wajen gudanar da tarbiyya ga iyalansa.
Sunana Maimu Shuraihu Jihar Kaduna:
Rrashin tausayi ne, sabida don ransune wasu kuma sabida yadda aka rabu, kuma hakan yanasa yara su tashi ba su damu da iyayen maza ba. ta hanyan nasiha da nunawa mazan su ringa jan yaransu a jiki. Ni da shawarar da zan bada shi ne; mu yi hakuri da juna indai har aure ya hada to hakuri shi ne na mu, indai bai zama dole ba ayi hakuri kar a rabu. Sabida rayuwar yanzu mutum na tare da yaransa ya tarbiyya ya kasance balle babu su tare da babansu Allah ya sa mu dace.
Sunana Najib Muhd Magaji Sansani, Miga Jihar Jigawa:
Hakika wannan matsala tana faruwa musamman a tsakaninmu al’ummar hausawa wanda kuma hakan yana jawo tabarbarewar tarbiyya a lokuta da dama. Wasu lokutan rashin ilimi da kuma talauci suke jawo hakan, wanda kuma hakan ke jawo tabarbarewar tarbiyyar yara har ma su zama matsala ga iyayen da ma al’ummar da suke rayuwa da su ta hanyar aikata laifika da ma shaye-shayen miyagun kwayoyi. Magana ta gaskiya sai an dage da neman ilimi musamman ilimin addinin musulunci ta haka ne za a san matsayin tarbiyya a rayuwar yara da kuma hakkin yara akan iyaye domin sauke shi yadda ya dace. Ya kamata mutum ya sani tarbiyyar yara a wajen iyaye wajibi ce, don hakan hakki ne daya rataya a wuyan uwa da Uba, don dole ne ya yi iya kokarinsa wajen tarbiyya ya kuma dage da addu’a.
Sunana Zainab Abdullahi (Lailat) Jihar Katsina:
Maganar gaskiya ba su kyautawa, domin kuwa ragamar kula da iyali gaba daya nauyi da Ubangiji ya rataya shi a wuyan Maza. Tun farko idan ka san ba za ka iya daukar wannan nauyi ba, bai ma kamata ka tunkari aure ba. Wasu Mazan talauci ne kan saka su sakin ragamar kula da yara zuwa ga uwa mace. Akwai gidajen da Mata ke daukar ɗawainiyar gidan, ita ce cin su, ita ce shan su, ita ce sauran bukatunsu na yau da kullum, mai gidan baya iya tabuka komai. To tabbas a irin wadannan gidajen an fi samun irin wadannan matsalolin. Wata uwar ita ke hana uba yin katabus akan yaran, da tunanin ba abin da yake tsinana mu su bare ya yi iko da su, wasu kuma Mazan ne da kansu kan yanke hukuncin hakan. Akwai matsala babba a yawancin irin wadannan gidajen. Babbar matsalar ita ce tabarbarewar tarbiyya, da karancin kunya. Ya zama dole kowanensu ya san hakkin da ke kansa. A matsayinka na uba ka sauke nauyin da Ubangiji ya dora maka, kada ka sakarwa uwa ragamar kula da gidanka da ‘ya’yanka, domin ita ma a karkashinka take, kuma ita kanta kula da ita da tarbiyyarta wajibinka ne. Allan ya sa mu dace.
Sunana Muhammad Sunusi daga Maiduguri:
Ni shawarar da zan bawa iyaye maza shi ne; su daina barwa mata tarbiyyar yaron musamman yara maza, saboda tarbiyyar yaro namiji sai namiji.
Sunana Sadik Abubakar Abdullahi C.E.O Lafazi Writers ‘Yammata, Rijiyar Lemo, Jihar Kano:
Hakika wannan matsala ce babba, kuma tana yawaita sosai musamman a wannan zamani da muke ciki. Akwai dalilai da ke sawa wasu mazan su ke aikata wannan abu. Na farko dai akwai rashin sanin hakkin su yaran a kan shi uba, ba ma yaran ba hatta ita uwar da ake bari da yaran hakkin tarbiyantar da ita yana wuyan shi mijin. Wajibi ne ya kula da tarbiyyarta da ta yaranta duka. Daga cikin matsalolin da hakan kan haifar ga yaran akwai rashin cikakkiyar tarbiyya, babu shakka yaran za su rika yin wasu abubuwan na reni da ba su dace ba, kuma ba za su yi kima a idon al’umma ba. Shi ma uban za a rika yi masa kallon wanda ba shi da kamala ta zama uba, tunda bai iya kulawa da tarbiyyar yaransa ba. Shawarata ga masu irin wannan hali ita ce, su ji tsoron Allah; su tsaya tsayuwar daka a kan dukkan hakkokin yaransu da matansu, kuskure ne babba a ce mutum ya sakar wa matarsa dari bisa dari ragamar kula da yaran da suka haifa. Su tuna fa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fada cewa; “Dukkaninku makiyaya ne, kuma za a tambaye ku game da kiwon da Allah Ya ba ku.”
Allah Ya sa mu dace.
Sunana Bilkisu Muhammad:
Annabi sallahu alaihi wasallam ya ce “kullukum ra’in wa kullum mas’ulu’an ra’iyyatihi”, wallahi ‘ya’ya amana ce kuma wallahi sai Allah ya tambaye ku akan amanar da Allah ya baku, maza ku ji tsoran Allah wallahi, wasu babu ce, wasu kuma kawai ganin dama ne, kuma hakan yanada illa wallahi, dan uwa idan ta gari ce duk inda za ta shiga ta nemo za ta yi, don ganin ta rufawa kanta da yaranta asiri. Idan aka samu uwa ba ta gari ba to da ita da yaran za su bi wata hanyar ta banza dan ganin sun samu abin da za su tafiyar da rayuwar su, uba ka sani wallahi duk zunubin da suka dauka kanada kamasho, Allah ya sa a gyara.
Sunana Lawan Isma’il (ABU AMFUSAMU) Jihar Kano Rano LGA:
Irin haka sam! baya dacewa, domin maza masu irin wannan halin bai ma kamala ace su yi auren ba, idan ma sun yi to haihuwa bata dace da su ba, ba don dai Allah ne mai badawa ba. Ire-iren wadannan mazan da ba sa iya kula da yaransu ko kuma daukar nauyinsu bai ma kamata suna amsa sunan mazaje ba, kuma ai ma’aiki (SAW) ya ce “kuyi aure ku hayayyafa domin nayi alfahari da ku ranar gobe kiyama” to kada ka kasa kula daukar nauyin yaranka kayi zaton kana cikin wadanda ma’aiki zai yi alfahari da shi ranar gobe kiyama. Hanyoyin magancewa akwai su da dama amma wadda tafi dacewa ita ce; kai namiji magidanci ka sani amana ce Allah ya baka akan iyalanka, kuma kiwo Allah ya baka tunda ka san za ka mutu to wallahi Allah zai karbi wannan kiwo da amanar da ya baka na yaran naka dama matan naka. Shawarata anan ita ce mu ji tsoron Allah a duk halin da muka tsinci kanmu, sannan mu sani kuma muna duba iyayenmu su ba haka suka yi mana ba, domin sakin layin iyaye da kakanni duk shi ne ya kawo tabarbarwar da muke akai yanzu, Allah ka shirya mana zuriya ameeen.
Sunana Abdullahi usman, Damaturu Jihar Yobe:
Wannan lamari kaso 90% cikin 100% na maza na aikata hakan wa marathonsu/’ya’yayen su. Mugunta ne da kuma rashin sanin mene ne hakkin daya ratya a a gere su. Abin da zai haifar shi ne; su ma yaran ba su ganin darajar iyayensu maza, ko kan iya jefa yaro wani hali wanda ya saba wa addini ko makamancin haka. Su iyayen su nemi ilimin addini dana zamani farko shi zai warware wannan matsalolin ta kowacce fuska. kai ma Namiji kasan meye ya kamata kayi matsayinka na me fada a ji a gida. Mata; a rage nunawa yaro kauna wanda bata kawo hanya mai bullewa.
Sunana Abdulkadir Ibrahim AKA Abdul, Jihar Kano:
Da farko dai ba shakka duk lokacin da maigida ya sakarwa uwar gida nauyin iyali, daka nanne fa girma ya fadi, domin dai Allah ya dora maka wannan nauyin, aure gaba ya dogara ne wasu manyan sharidai akan namiji kamar haka, Ciyarwa, tufatarwa, ilimantarwa da kula lafiyar iyali, su kuma yaran ko zuri’ar da aka samu, Allah ya ce; abin kiwo aka baka, kuma za a tambayeka. Duba da haka wajibi ne akan uba ya ciyar, ya tufatar, kula ilimunsu da lafiyarsu da basu tarbiyya har su kai munzalin girma wato su balaga kana ya aurar da su, akasin yin haka ne yake haifar mana da matsala, domin su mata dai raunanane sakar musu ragama, illa ce, duk da talaucin da ake ciki yanzu yana taka rawar wannan matsala, amma a fahimta shi ne wasu mazan jahilcin rashin sanin hakkin daya rataya akansu yana taka mahimmiyar rawa, wasu kuma san rai ne, sani ya kamata wasu su nema akan zamantakewa ta aure kafinma su yi, na biyu ya kamata har hukuma ta shiga al’amarin, domin wallahi wasu na bukatar tsawatarwa, ba yadda za a yi mutun da babzai iya rike mace 1 ma da ko ‘ya’ya 2, amma ya tara mata 3-4 da yara da yawa, kuma a sami saka mako mai kyau.