Labarin da muke samu da ɗumi-duminsa na cewa Da mai martaba Ohinoyi na ƙasar Ebira y rasu .
Mai martaba Ohinoyi, Alhaji Ado Ibrahim wanda har ila yau shi ne mataimakin shugaban Jama’atu Nasril Islam (JNI) na kasa, ya rasu yana da shekaru 94.
A yau ake sa ran za a yi jana’izarsa a fadarsa da ke birnin Okene, a Jihar Kogi. Allah Ya jikansa da rahama.