Babban bankin Nijeriya (CBN) ya bukaci wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta yi watsi da karar da lauyan kare hakkin dan Adam, Femi Falana ya shigar na neman tilasta babban bankin ya dakatar da faduwar darajar Naira.
Amma CBN ya ki aamncewa da karar, inda ya ce, Falana ba shi da hurumin shigar da karar kuma kotu ba ta da hurumin sauraron karar.
- Kwarewar Sabon Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN)
- Akwai ‘Yan Cin Tofa Albarkacin Baki A Gwamnatin Tinubu – Minista
Babban Lauyan dai ya shigar da karar ne domin kalubalantar faduwar darajar Naira kan dalar Amurka.
A karar mai lamba FHC/L/CS/470/23, Falana yana neman kotu ta ba da umarnin dakatar da CBN daga amincewar bankin cewa, yanayin kasuwa ne zai tabbatar da darajar Naira da kuma farashin canjin Naira da sauran kudade kamar yadda sashe na 16 ya tanada na dokar babban bankin kasa.
Ya kuma bukaci kotun da ta tursasa CBN ya dakatar da batun dalar Amurka wajen tattalin arzikin kasar tun da sashe na 20(1) na dokar Bankin ya nuna cewa, Naira ce kadai kudin da aka amince a yi hada-hada da ita a Nijeriya.
Mai shigar da karar, ya roki kotun da ta bayyana cewa, a sashe na 16 na dokar babban bankin kasar, kudin da Nijeriya ta amince da shi, shi ne Naira da kobo, don haka, in aka hada sashi na 15 da na 20 (1) na dokar babban bankin kasar, dole wanda ake tuhuma (CBN) ya tabbatar da dokar cewa, amintattun kudin hada-hada a Nijeriya, takardun Naira ne kawai.