Tun daga lokacin da zuwa yanzu, nazarin sararin samaniya na zama aikin da Sinawa ke kokarin rayawa. A kasar Qi ta lokacin Zhanguo, wato a karni na 4 kafin haihuwar annabi Isa, masu bincike sararin samaniya da aka kira Gande da Shishen, sun rubuta littafi mai suna “Ilmin Taurarin Sararin Sama na Gan-Shi”. Wannan ne littafi na farko a fannin nazarin sararin samaniya da taurari a kasar Sin, har ma a duniya baki daya. Daga bisani, masana da yawa a fannin ilimin taurari, su kan yi amfani da alkaluman dake cikin wannan littafi a yayin tabbatar da matsayin rana, da duniyar wata, da taurari, da kuma hanyoyin da suke bi. Shi ya sa littafin “Ilmin Taurarin Sararin Sama na Gan-Shi” na da muhimmanci kwarai da gaske a tarihin nazarin sararin samaniya da taurari na Sin da na duniya.
Sinawa a yanzu, sun gaji hikima, da wayewar kai daga kaka da kakanni a wannan fanni, har suka cimma burin kakanninsu na kai ziyara a sararin samaniya, wanda ba za su yi a lokacin da ba. Kwanan baya, kasar Sin ta harba kumbon Shenzhou 17 mai dauke da ’yan sama jannati. A cikin shekaru 20 da suka gabata, kumbon Shenzhou ya cimma kaiwa da kawowa sau 10 daga doron kasa da sararin samaniya, da kai ziyara zuwa sararin samaniya sau 12. Harba irin wadannan kumbuna na taimakawa Sin a fannin hadin kanta da kasashen duniya don nazarin sararin samaniya, da ingiza bunkasuwar kimiyya da habaka tawagogin masu nazari.
Saurin bunkasuwar kimiyyar zirga-zirga a sararin samaniya ta Sin na ingiza bunkasuwar wasu sabbin sha’anoni, ciki hadda sabbin makamashi da kayayyaki. A nan gaba, ilmin zirga-zirga a sararin samaniya na Sin zai ciyar da bunkasuwar sha’anin yanayin sama, da ilmin kimiyyar kere-kere a sararin samaniya, da ilmin duniyar wata, da taurari, da ilmin duniyar kasa a sararin samaniya da sauransu.
Ban da wannan kuma, ana iya amfani da tashar sararin samaniya da Sin ta kafa da dai sauran dandaloli wajen ci gaba da nazarin kimiyyar zamani dake da amfani ga bil Adama da cimma karin nasarori, ta yadda Sin za ta taka rawarta wajen ingiza kokarin da Bil Adama ke yi na amfani da sararin samaniya cikin lumana. (Mai zana da rubuta: AMINA)