Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce Sin za ta zurfafa aiwatar da matakan kare ikon mallakar fasahohi, ta yadda za ta kai ga matsayin koli a fannin mallakar fasahohi, domin samar da ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire.
Li Qiang, ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin zaman nazari na majalissar gudanarwar kasar Sin. A cewar sa, aiwatar da matakai masu nasaba da wannan buri na da matukar muhimmanci, wajen karfafa ikon kasar a fannin inganta takara, da fadada bude kofa mai karko.
- An Gudanar Da Taron Tattaunawa Kan Raya Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Tsakanin Sin Da Girka
- Kamfanonin Sadarwa Na Kenya Sun Yi Hadin Gwiwa Da Na Sin Don Kaddamar Da Kamfanin Hada Wayoyin Hannu
Firaministan na Sin ya kara da cewa, domin samun cikakkiyar nasarar kirkire-kirkire, dole ne a kara azama wajen ingiza kafuwar tsare-tsaren dokoki, da salon jagoranci, da manufofi, a kuma samar da dokoki masu dacewa da sabbin fasahohi, ta yadda za a kai ga kafa ginshikin bude sabuwar turbar bunkasa masana’antu.
Daga nan sai ya bayyana muhimmancin rungumar musaya, da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a fannin kare ikon mallakar fasahohi, da kuma tsara dabarun warware sabani da ka iya bijirowa a fannin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)