Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya rantsar da Natasha Akpoti-Uduaghan a matsayin Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da zaben Akpoga-Uduaghan, wadda kotun sauraron kararrakin zabe ta majalisar dokokin Kogi ta tabbatar, a ranar Litinin.
- Kotu Ta Dakatar Da Majalisar Dokokin Ribas Daga Tsige Fubara
- Yadda Na Sha Mugun Duka A Hannun ‘Yansanda — Ajaero
Abokin hamayyarta kuma dan takarar jam’iyyar APC, Abubakar Ohere, ya kalubalanci nasarar da ta samu a kotun.
Kotun daukaka kara, a hukuncin da ta yanke ta amince da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke, inda ta bayyana ‘yar takarar PDP a matsayin sahihiyar Sanatan Kogi ta Tsakiya da kuri’u 54,354, yayin da dan takarar APC, Ohere ya samu kuri’u 51,291.
Magatakardar majalisar dattawa ne ya rantsar da ita da misalin karfe 11:41 na safe.