Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce kasarsa za ta ci gaba da goyon bayan cikakken ‘yanci da ikon kasar Sudan kan yankunanta.
Wang Yi, wanda kuma shi ne daraktan hukumar kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS, ya bayyana haka ne a yau Alhamis, yayin ganawarsa da Malik Agar, mataimakin shugaban gwamnatin riko na kasar Sudan.
Wang Yi ya kuma bayyana goyon bayan Sin ga Sudan wajen cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kasar, da kuma lalubo hanyar ci gaba da ta dace da yanayin da take ciki.
- Hukumar Alhazai Ta Jihar Kebbi Ta Samu Sabon Shugaba
- Akpabio Ya Rantsar Da Natasha Akpoti-Uduaghan A Matsayin Sanata
Ya kara da cewa, ba tare da la’akari da sauyin da za a samu ba, matsayar kasar Sin na raya dangantaka da Sudan, ba za ta sauya ba.
A nasa bangare, Malik Agar, ya ce Sin ta zama abar koyi ga kasashe masu tasowa, yana mai jaddada cewa, Sudan za ta inganta raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ba tare da barin wani daga waje ya tsoma baki ba.
Har ila yau, ya ce Sudan na daukar rawar da Sin ke takawa a harkokin kasa da kasa da muhimmanci, yana mai godewa Sin din bisa yadda take mayar da hankali kan yanayin kasarsa. (Fa’iza Mustapha)