A ranar Juma’ar nan dakarun tsaron hadin guiwa da suka hada da sojojin Nijeriya da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun yi nasarar dakile wani harin da cafke wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan ta’addar Kungiyar Boko Haram ne a Kano.
Kakakin rundunar, Brig-Gen. Onyema Nwachukwu, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce sojojin sun kai wani sumame maboyar ‘yan ta’addar da sanyin safiyar Juma’a 3 ga watan Nuwamba 2023 a karamar hukumar Gezawa da ke jihar Kano.
- Masu Kwacen Waya 5 Sun Shiga Hannun Jami’an Tsaro A Kano
- Rashin Tsaro: An Yi Saukar Alkur’ani 2,444 A Kano
Onyema ya ce, an kai farmakin ne kan ‘yan ta’addar da nufin da cafke su don dakile wani mummunan harin da Boko Haram din ke shirin yi a Jihar Kano.
Kakakin ya ce, sojojin sun samu nasarar cafke wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan ta’addar Boko Haram ne wanda yanzu haka suke tsare a hannun jami’an tsaro, rundunar hadin guiwar ta yi nasarar kwato bindigu kirar AK 47 guda biyar, da karin wata bindiga daya da Bama-bamai guda biyar da gurneti na hannu guda shida da kayan Sarki (Uniform) kala daban-daban guda biyar da wasu jakunkuna na guda 10 da wasu kayan ƙera kayan fashewa (IED).
Kakakin ya ce, rundunar ta hadin gwiwa tsakanin sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro na gudanar da aikinta don dakile ta’addancin ‘yan ta’adda da sauran matsalolin tsaro.