Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana a yau Juma’a da firaministan Girka, Kyriakos Mitsotakis a birnin Beijing. Yayin ganawar, shugaba Xi ya ce, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu cikin sama da rabin karni, Sin da Girka sun yi ta raya dangantakar cikin aminci da juriya.
Ya ce, a shirye Sin take ta inganta hadin gwiwar dabarun ci gaba da Girka, da zurfafa hadin gwiwa a fannonin sufuri da jiragen ruwa da makamashi da sadarwa da hada-hadar kudi da fadada damarmakin hadin gwiwa a fannin bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da inganta hadin gwiwar shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” tare da samar da gaba mai karko da dorewa na tashar ruwa ta Piraeus
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Gudanar Da Babban Taron Birane Masu Sada Zumunta Na Sin Da Amurka
- Xi Jinping Ya Jaddada Muhimmancin Samar Da Kyakkyawar Fahimtar Al’ummantaka Ga Jama’ar Kasar Sin
A nasa bangare, Kyriakos Mitsotakis ya ce, a shirye kasarsa take ta ci gaba da inganta hadin gwiwar shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da kasar Sin, da kara ci gajiya da fadada damarmakin hadin gwiwa a fannonin jiragen ruwa da sufurin jiragen ruwa da makamashi mai tsafta, tana mai fatan karin kayayyakin kasar za su shiga kasuwar kasar Sin tare da maraba da masu yawon bude ido na Sin a Girka.
Sannan, shugaba Xi Jinping ya kuma gana da shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz yau Juma’a ta kafar bidiyo.
A cewar Xi Jinping, a yanzu haka, cinikayya tsakanin Sin da Jamus na samun ci gaba yadda ya kamata, kuma yawan jari a tsakaninsu ma na karuwa, baya ga dangantakarsu dake kara kyautatuwa da kara karfi da samun nasarori.
Sama da kamfanonin Jamus 130 ne za su halarci baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin CIIE karo na 6, wanda ke nuna kwarin gwiwar da kamfanonin Jamus din ke da shi kan ci gaban Sin. Ana kuma fatan bangaren Jamus zai nace ga fadada bude kofar hadin gwiwa ga kamfanonin kasar Sin.
A nasa bangare, Olaf Scholz ya bayyana ra’ayin kasarsa game da rikicin Palasdinu da Isra’ila, yana mai fatan ci gaba da tuntubar juna tsakanin Jamus da Sin kan batun.
Game da hakan, Xi Jinping ya ce idan ana son warware tushen rikicin Palasdinu da Isra’ila ko kuma rikicin Ukraine, to akwai bukatar yin tunani mai zurfi a bangaren tsaro, da nacewa ga samar da cikakken tsaro na bai daya cikin hadin gwiwa da samar da ingantaccen tsarin tsaro mai dorewa kuma bisa adalci. (Fa’iza Mustapha)
(Fa’iza Mustapha)