Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi kira da a sassauta rikicin dake faruwa a tsakanin Isra’ila da Falasdinu, da ma ganin an tsagaita bude wuta a Gaza.
Wang, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bayyana hakan ne, a yayin tattaunawa ta wayar tarho da mataimakin firaministan kasar Jordan kuma ministan harkokin wajen kasar Ayman Safadi jiya Alhamis.
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Gudanar Da Babban Taron Birane Masu Sada Zumunta Na Sin Da Amurka
- Dakarun Tsaron Hadin Guiwa Sun Dakile Harin ‘Yan Ta’adda Da Cafke Mutum 2 A Kano
Wang ya ce, kasar Sin ta yi kakkausar suka ga hare-haren da ake kai wa sansanonin ’yan gudun hijira a zirin Gaza. Yana mai cewa, rayuwar al’ummar Falasdinu da Isra’ila duk muhimmancinsu daya, kuma bai kamata a rika nuna fuska biyu ba.
Wang ya jaddada cewa, kasar Sin tana goyon bayan muhimman shawarwarin da kasashen Larabawa suka gabatar game da tsagaita bude wuta, da wanzar da zaman lafiya. Ya ce, a matsayinta na shugabar karba-karba ta kwamitin sulhu na MDD na wannan watan, a shirye kasar Sin take ta ci gaba da yin cudanya da hadin gwiwa da dukkan bangarori, da yin duk mai yiwuwa wajen samar da daidaito a kwamitin sulhu, domin ganin an kwantar da hankula cikin gaggawa.
Ya ce da farko, ya kamata mu yi kokarin ganin an tsagaita bude wuta da kuma tabbatar da kai agajin jin kai ba tare da wani cikas ba. A halin da ake ciki kuma, ya kamata a hanzarta kiran taron zaman lafiya na kasa da kasa, don cimma sabon matsaya kan sake farfadowa da aiwatar da shawarwarin neman kafa kasashe biyu, da tsara takamaiman jadawalin lokaci da taswirar aiwatar da abubuwan da aka kai ga cimmawa.
A nasa bangare kuwa, Safadi ya godewa kasar Sin, bisa kokarinta na tabbatar da daidaito da adalci kan batun Falasdinu, da kuma goyon bayan kudurin da aka gabatar a taron gaggawa da babban zauren MDD ya kira. (Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya)