Bisa zargin aikata ba daidai ba, lokacin gudanar da zaben kujerar dan majalisar dattawa mai wakiltar Adamawa ta kudu, ‘yan takara 5, sunki amincewa da sakamamon zaben fidda gwanin bisa zargin ba’abi ka’ida ba.
‘Yan takaran biyar, sun roki kwamitin gudanar da zaben da ta sanar da Adamu Isma’ila Numun da cewa ya lashe zaben, da ta soke takaransa, bisa cewa ya karya dokar zabe, da sayen kuri’u, don haka bai cancanci tsayawa takaran ba.
Da su ke magana da ‘yan jaridu a Yola, ‘yan takaran Baresta Bala Sanga, Bridget Zidon, Grace Bent, Sani Jada, Ahmad Abubakar, sun tabbatar da cewa basu shiga zaben da’akace Adamu Isma’ila ya lashe zaben ba.
Da yake magana amadadin ‘yan takaran Baresta Sanga yace “bukatarmu shine su yi amfani da takardar da muka basu ranar 29 ga Mayu 2022, cewa Adamu Isma’ila Numun, bai cancanci takara ba, saboda sayen kuri’un da yayi, lokacin zabe.
“Wannan abin kunya ne ga jam’iyya, a kafa wani kwamitin da zai gudanar da sabon zabe, kuma a canja wurin gudanar da zaben, daga Numan zuwa inda ya dace a yankin.
“Mun gaskata jam’iyyar APC zata gudanar mana da adalci, duk da ba’a da kaskancin da Adamu Isma’ila Numan, ya shigo dashi, bamu cire tsammani ga bukatunmu ba, muna zaman jiran mu bayyana gaban kwamitin amsar koke” inji Sanga.
‘Yan takaran sun kuma bayyana cewa ba’ayi zaben fidda gwani a yankin ba, ya kamata a gudanar da zaben a ranar 29 ga Mayu 2022, duk mu bama wurin, mu munyi imanin an tsara ne da raba mana kuri’un.
“Mafiya yawan masu zabenmu sun koma garuruwansu, kuma gurare ne mai nisa, kusan mutum zaiyi awa 4, abune da ba zai yiwu ba ka taro duka masu zabe, duk da babu masu zabemmu da masu sa mana ido, a zahiri ci gaba da zabe a haka abin kunya ne.
“A irin wannan zaben fidda gwanin da takardar kada kuri’a, da duk ‘yan takara, da masu sa ido, za su amince, mu ‘yan takara da masu sa mana ido bamu a wurin zabe, sunyi abinda ya musu ne kawai.
“Muna bukatar kwamitin sauraren koke-koken zabe ta lura da wadannan manyan batutuwa wadanda suke nuna makurar rashin adalci, an tura mana sako karfe 8:54 na safe cewa za’ayi zaben 12 na rana.
“Kawai awanni uku da mintuna 6 aka bamu, mu shirya a yi zaben fidda gwanin, yaushe zamu tattaro kan masu zabenmu? Wannan wani irin makoran rashin adalci ne” inji Sanga.
Da yake maida kalami kan zargin da ‘yan takaran sukayi Adamu Isma’ila Numan, yace “kawai don basu sukayi nasara bane, dabi’ace ta wanda ya fadi zabe
“Tunda farko mun yarda masu sa mana ido, su taimakawa wadanda basu iya rubutu ba, lokacin da mai sa mini ido zai taimaki mai zabena, suka fara cewa sayen kuri’u sayen kuri’u.
“Ni bansan komai akan haka ba, ni ban umurci wani ko wasu su dauki doka a hannu amadadina ba, amma aka dakatar da zaben.
“Lokacin da’aka sanar za’ayi zabe, na nemo masu sa mini ido da masu zabe, mun tafi wurin zabe mukayi zabe kuma munci zaben” inji Numun.