Hajiya Hafsa Sale, matashiya ce da ta samu kwarewa a fannin sarrafa kwamfuta wacce kuma take gudanar da ayyukanta da take samun kwabo da dari ta hanyar amfani da fasahar sadrwar zamani. Ta bayyana wa LEADERSHIP Hausa yadda take tafiyar da rayuwarta cikin sauki. Kazalika ta ba wa mata magidanta shawara a kan yadda za su iya neman kwabo da dari a cikin gidajensu ko da kuwa mazajensu ba su da ra’ayin barin su fita aiki. Bugu da kari, ta tabo irin kalubalen da ‘yan mata ke fuskanta a wannan zamanin tare da bai wa duk wani da namiji da yake da kanne mata shawarar yadda za a shawo kan matsalar.Ga dai yadda hirar ta kasance: Â
Da farko, da wa muke tare sannan yaya tarihinki a takaice?
Eh to a takaice dai sunana Hafsat Isa Sale. An haife ni a garin Jos Jihar Filato, amma kuma ban taso a Jihar Filato ba, ina makarantar firamare na koma Jihar Kano, inda a nan na ci gaba da karatuna har na zo na samu na yi aure na ci gaba da karatuna na yi Diploma a Business Admin, a Jihar Delta, daga na dawo Arewa na koma na karanci Health Education wanda a yanzu kuma saboda zaman gida da kuma danne-dannen waya inda na kara ilimin Animation wanda har yanzu nake yi irinsu Graphic Design da sauransu, har na yi training dina na Elastration, wannan kenan.
Kin yi karatu ga kuma abubuwa da dama kina yi, Hajiya takamaime, mece ce sana’arki?
Ni sana’ata duk wani abu da ya shafi Logo, Editing na duk abin da ya shafi bidiyo da kuma gyara bidiyo da kuma duk abin da ya shafi waya da na sana’o’i da sauransu. In na ce kuma Animation, ina nufin Cartoon kenan ina iya yin abubuwa kamar TB Animation, sannan harkar kiwon lafiya, ina nufin duk wani abu da zai hana ka kamuwa da ciwo, misali a ce wannan abin zai iya kawo maka ciwo a cikin jikinka ko kuma zai kawo maka matsala a cikin jikinka da cututtuka na duniya da na rayuwa dai haka irin wadannan abubuwan. Idan kuma na ce Columnist ma’ana ina dan rubuce-rubuce wanda ake wallafawa a LEADERSHI Hausa.
Me ya sa kika rungumi sana’o’in da kike?
Eh to, a nan zan ce duk wani abu da zan fada da nake yi mata za su iya yin sa, dalili kuwa shi ne duk abubuwan da nake yi ba sai mace ta fita ba, a cikin gidanki za ki iya yin sa. Animation kina cikin gida za ki yi kuma ki samu ki sayar. Akwai website da ake da shi wanda duk wani abu da kika yi za ki je ki sayar da shi a wannan shafin, idan kuma za ki yi cartoon dinsa ne ma ko ki je ki yi tallansa ga mutum na wani kasuwanci duk za ki iya yinsa. Idan kuma aka ce graphic design kamar su Logo fulayas na sana’o’i wanda za ki yi wa wani ya biya ki ta website kenan ko kuma ta WhatsApp, mutum zai biya ki kudinki ki je ki masa aikinsa ya biya ki. Sai kuma idan na ce Columnist za ki yi ga ki nan a zaune a cikin gida, za ki yi rubuce-rubucenki mai ma’ana ki tura a buga, kin ga nan ma kina gida ba tare da kin fita ba. Idan kuma na ce Elocutionist, kin gama training dinki, don ana training online yadda za ki gyara Turancinki duk akwai su, yadda za ki koyi turanci tun daga farko, idan kika gama koya, wannan za ki janyo mutane online kina karbar kudinki sannan kina aikinki, to kin ga a nan ma ba sai kin fita ba. To ta nan kenan duk wani abu da nake yi tun da ni ma ba na fita kowa ma zai iya yi.
Ya kike ganin rayuwar mata a zamanin nan?
A duniya kowa da abin da yake so, da farko dai burina shi ne in zama likita, da Allah bai cika min wannan burin ba sai na koma bangaren lafiya na yi Heath Education na karanci abin da ya shafi lafiya, sannan kuma ina tafiya har na zo ina sha’awar Turanci, nan na shiga na zama Elocutionist, sannan kuma ni mai son danne-dannen waya ce, sai na ga to idan ina danne-dannen waya babu abin da nake karuwa da shi, wannan ya kai ga sha’awar nima in fara yin irin wadannan abubuwan, na zo kuma na ga Animation yana birge ni sosai da sauransu sai na ce kai ni ma bari dai zan iya zama wannan abin, to wannan sha’awar abin sai nima na zo na zama ina yi.
Me ya kamata maza su gyara a zamantakewar aure?Â
Eh to zan iya cewa a zamantakewa shi ne namiji yana da kyau ya aminta da matarsa, idan har ka san wa ka aura ya kamata ka aminta da ita, ka ba ta yarda ku yarda da junanku ba zargi ko wani abu, to wannan ina ganin shi zai ba ta damar ta samu ci gaban da take so a rayuwarta wanda zai amfane ka ya amfane ta kuma ya amfani ‘ya’yanta, don in ka ilmantar da mace kamar ka ilmantar da al’umma ne. To sai ka ga kafin ta ilmantar da al’ummar ita ta ilmantar da ‘ya’yanta na cikin gida, to wannan abu taimakonka ne taimakonta ne taimakon kowa.
Da yawa na ganin ‘yan mata a halin yanzu ba su samun mazan aure da wuri, ko kin yarda da hakan?
Eh to zan iya yarda, kasancewar yanzu gaskiya muna da ‘yan mata sosai wadanda ba mazan aure, kuma wannan sai in ce duka a bangarorin ya danganta da harkokin rayuwarsu da kuma irin rayuwar da ake yi a wannan zamanin saboda sauyin rayuwa da aka samu a wannan lokaci. A da za ka ga da yarinya ta kai shekara 13-14, an fara tunanin aurar da ita, amma yanzu za ka ga yarinya sai ta kai shekara ishirin da, wata ma tun tana shekara 17 maza za su fara zuwa suna son ta da aure, amma saboda wasu bukatu ko kuma wani abu nasu na daban za ka ga sun ce sai sun gama wani abu ko sun kai wani matsayi dai, wanda a nan zan iya cewa har da maza ma suna taka rawa a cikin wadannan matsalolin da ake fuskanta na yammata.
Saboda za ka ga namiji kana wa (yaya) kana da kanne mata, sau tari za ka ga mazan ba su san larurar ‘yan uwansu mata ba, wani bai sana’a, ba a dora shi a kan hanyar da zai ce ya fara aiki har ya fara samun kudi, irin ya ce bari ya sa wa ‘yar uwarsa kudin kati, ko ya saya mata audugar al’ada ko wani abu dai da ya shafi rayuwarta wanda kuma an san ita mace ‘yar kwalliya ce, to idan ba a ba ta a cikin gidansu ba a ina za a bata?
Wannan tambaya ce mai muhimmanci sosai, ya za ta yi idan ba a ba ta a gidansu ba, wanta bai dauka ya ba ta ba, mahaifi a matsayinka na mahaifi ba ka dauka ka ba ta ba, hala tun yarinyar nana tana karama kuka take wa mahaifiyarta ta ba ta ko kar ta ba ta, ba damuwarka ba ce, ba ta san a saya mata hoda ta saya mata irin kayan kwalliyar nan da ya kamata a ce ‘ya mace ta yi ba sai dai a waje za ta ga ‘yan mata suna saka kaya suna rike babbar waya, kai ba ruwanka tun da ba ‘yarka ba ce ko kuma ba matarka ba ce, wanda kuma a gida ka riga ka gina wannan ‘Foundation’ din da wannan yarinyar in ba a ba ta ba dole za ta nema, dole idan wani saurayi ya zo ya ce ta bi shi ya dauke hankalinta, kuma ka ga kenan ka kirawo abu daban ya zo ya sa mata wani ra’ayi na daban da ita ma kullum sai ta yi abu kaza kafin ta samu abin da take so da sauransu. To irin wadannan ina ga yana daga cikin abin da ya sa ‘yan mata suka yi yawa a gari ba mazajen aure.
Maganar farko in ana so a gyara wannan matsalar, yana da kyau iyaye mata su san abubuwan da ya kamata su dinga yi, sannan kuma maza su dau abin da Allah ya dora musu, ma’ana su sauke hakkokin da ke kansu, ka kula da ‘ya’yanka mata, sannan ka kula da matar da take gida, kar ka rika kallon mata a waje suna saka kaya suna saka turare suna kwalliye-kwalliye ka ce kai kuma a gidanka ka yi tsammanin ba ka bayar ba za a yi maka. To in ka kula da wannan, na cikin gidan in suna kulawa da wadannan, za a samu ci gaban da in kana bayarwa wannan yana bayarwa to ba za su dinga zuwa waje suna nema har ma wani namiji ya dinga yaudararsu ba. Idan kai a matsayinka na wa (yaya) kana kulawa da ‘yan uwanka mata ka san me suke so ka san matsalolinsu, kuma ka yarda da cewa idan ba ka ba su kaza ba za su nema a hannun wani, kai ma kenan ka karantu ta wannan fannin, ba za ka je ka lalata ‘ya’yan wasu ba, saboda me, kai ma ka san kana da ‘yan uwa kuma kai ma ka san me suke bukata a rayuwarsu, idan ana kula da wannan fannin kam za a samu gyara sosai.
Me kika fi sha’awa a abinci?
Gaskiya ni na fi son duk abun da yake da wake, misali Alala, ko kuma shinkafa da wake da mai da yaji kasancewata Bakanuwa wacce na girma ma dai a Kano zan ce tun da ba a nan aka haife ni ba kusan na dai zama Bakanuwar kenan, to ina son shinkafa da wake da mai da yaji da faten wake da duk wani abu da ya shafi wake ina sonsa
To fannin abin sha
A fannin abin sha babu abin na fi so irin Pepsi
Wace kala ta fi ba ki sha’awa?
Kalar da ta fi bani sha’awa ita ce ruwan kasa da shudi
Mene ne fatanki ga matan Arewa?
Fatana ga matan Arewa shi ne ina yi musu fatan alheri kuma su san me suke ciki, lokaci ya kawo na an daina zama, ki nema kudi a cikin dakinki lokaci ya yi da mata za su nemi kudi a dakunansu, kar ki ce wai ba zai bar ki ba shikenan, ki rike wannan ki zauna a daki ki ce ke ba za ki nemi wata sana’a ba, sana’a ba sai kun fita ba yanzu, kina rike da waya 24/7 kina hira me kike amfana da shi, ki nemi abin da zai dauke miki hankali, ki shiga graphic design din nan gashi ana koyar da shi a online, shi kansa ilimi yanzu ba sai kin fita kin je kina neman inda za ki karanta ba gashi nan a soshiyal midiya kawai biya za ki yi ki fara karatunki, kafin ki ce meye kin fara kin fara amfanar kanki da ‘ya’yanki.
Akwai sabon shiri na Madubin rayuwa na LEADERSHIP Hausa, da muka fara wanda zai dinga tabo batutuwan rayuwa, ta kowane bangare, soyayya zamantakewar aure, tarbiyya, girke-girke, gyaran jiki da sauransu. Me za ki ce game da wannan shiri?
Wannan shiri ne mai amfani, kullum burina in ci gaba da taimaka wa LEADERSHIP saboda suna fadakarwa kuma sun aba wa mata damar da za su san me suke so su sani da kuma maza kansu ana amfana kuma ana ilmantuwa da su, kasancewar duk shirye-shiryensu akan mata ne da kuma abin da ya shafi zamantakewar aure da sauransu, to ni a nan sai in ce ina goyon bayan wannan shirin saboda na san akwai ci gaba sosai, kuma duk inda zan taimaka in sha Allahu zan taimaka akan wannan shirin
Yaya sunan Kamfanin naki
Eh to ina da Mimssmartpurchase inda mutum zai dinga zuwa yana sayen Data ya sayar a wannan website din. Sannan kuma ina mimssmartpurchase.com.ng, inda nake saka ayyukana da kuma abubuwan da ya shafi Animation, har da koyo idan mutum yana so ya yi zai iya koya ta wannan hanyar, in mutum ya kira ni ma ya ce ina so zan koyi kaza nan da nan zan dora mutum a kan hanya yadda ya kamata.
Muna godiya
Na gode nima sosai.