Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa, hukumar ta nemi naira biliyan 18 daga kasafin naira tiriliyan 2.17 ne domin ta biya ma’aikatanta sama da 16,000 kuɗaɗen alawus ɗin da gwamnatin tarayya ta yi musu ƙari acikin 2023.
Yakubu ya ce, jama’a sun yi wa hukumar yarfen cewa ta kashe makudan kudi har naira biliyan 335 na kasafin 2022 a zaɓen 2023.
- Dalilan Da Suka Sanya Dole Nijeriya Ta Rungumi Fasaha Domin Bunkasa Tattalin Arziki
- Matar Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar Da Bada Tallafin N50,000 Ga Mata Dubu 4 A Gusau
Don haka, hukumar ta ce, naira biliyan 18 da aka ware mata a wannan kasafin ƙarshen 2023, ba a zaɓuɓɓukan gwamnonin Bayelsa, Kogi da Imo za ta kashe su ba kadai.
Da ya ke jawabi a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya a ranar Laraba, Yakubu ya ce, mafi yawancin kuɗaɗen duk wajen biyan ma’aikata za su tafi.
Yakubu ya ce, hukumar INEC na buƙatar naira biliyan 10.6 domin biyan ma’aikatanta ƙarin kashi 40 ciki 100 na alawus ɗin da Gwamnatin Tarayya ta yi musu. INEC na da ma’aikata 16,624.
Ya ce: “Za ku iya tunawa acikin watan Afrilu na wannan shekarar, an yi wa mai’aikatan gwamnatin tarayya ƙarin wasu kuɗaɗen alawus har zuwa kashe 40 cikin 100. To mu babu wannan ƙarin a cikin kasafin INEC na 2023, saboda an riga an rattabawa kasafin 2023 hannu a majalisa tun cikin Disamba, 2022. A watan Fabrairu gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar cewa an ƙara wa ma’aikatan gwamnati kashi 40 cikin 100 na alawus ɗin DTA da wasu alawus daban.
“INEC tana da ma’aikata sama da 15,000. Kuma a yanzu babu yadda za a iya samun kuɗaɗen da za a biya su, idan ba a bijiro da ƙwarya-ƙwaryan kasafin a ƙarshen wannan shekara ba.
“Dalili kenan muka gabatar da buƙatun kuɗaɗen ga gwamnati, don haka aka saka INEC cikin wannan kasafi.
Yakubu ya ci gaba da bayyana yadda hukumar zaɓe ta kashe naira biliyan 355 na cikin kasafin 2022, inda ya ce, akwai sauran kudaden a tare da hukumar.
Hukumar ta yi amfani da wani kaso na kuɗin wajen shirya zaɓen jihar Osun da Ekiti, yanzu kuma tana shirin gudanar da zaɓen Bayelsa, Imo duk da sauran kuɗaɗen.
Ya ce a yanzu sun nemi Naira biliyan 18 ne daga gwamnati saboda biyan ma’aikata alawus ɗin su da kuma biyan wasu sauye-sauye da aka samu na daga tashin farashin wasu kayayyaki a yanzu, kamar litar fetur, wadda aka kasafta ta akan naira 197 duk lita amma yanzu kuma ta haura Naira N600.