Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayar da ranar Litinin da Talata, 11 da 12 ga watan Yuli a matsayin ranakun hutu don gudanar da shagulgulan Sallar Layya a bana.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin gwamnatin tarayya mai dauke da sa hannun Babban Sakataren ma’aikatar, Shuaib Belgore a ranar Alhamis.
- Sallah: ‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Tawagar Shugaba Buhari Hari A Hanyarsa Ta Zuwa Katsina
- Babbar Sallah: Masarautar Katsina Ta Soke Hawan Sallah
“Ina kira ga al’umar Musulmi da su ci gaba da nunawa juna soyayya da rungumar zaman lafiya da kokarin kyautatawa juna kamar yadda yake koyarwar Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam),”
“Musulmi su kuma yi amfani da lokacin wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya da hadin kai da wadata da kwanciyar hankali da rokawa kasar nan zaman lafiya duba da kalubalen rashin tsaro da muke fuskanta a halin yanzu,” Cewar Aregbesola.