Shugaban hukumar Hisba ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce hukumar za ta aurar da ‘yan TikTok a jihar.
Ya bayyana cewar idan suna bukatar a yi musu auren gata a Kano, hukumar a shirye ta ke sai kowane daga cikin masu TikTok ya samu mace ‘yar TikTok a daura masa aura da ita.
Daurawa ya bayyana cewar ba wai sun kira su ba ne don cin mutunci ko tozarci, sun kira su ne domin ba su shawarwari akan wannan kafa ta sadarwa da suke amfani da ita.
Daga karshe shugaban na Hisba ya yi musu albishirin cewar akwai wasu hukumomi masu zaman kansu da ke da niyyar hada hannu da su domin tallata musu hajojinsu suna biyan su.