• English
  • Business News
Saturday, June 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 10, Sun Kwato Bindigogin AK47 Biyar Da Wasu Muggan Makamai A Kaduna

by Sulaiman
2 years ago
in Labarai
0
Sojoji
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A ci gaba da aikin fatattakar ‘yan ta’adda da rundunar sojin Nijeriya ke yi a Kaduna, ta ci gaba da samun nasara inda ta kashe ‘yan ta’adda 10 cikin mako guda tare da kwato makamai daga hannun ‘yan ta’addan.

A cewar wata sanarwa da mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya, Laftanar Kanar Musa Yahaya ya fitar, ya ce, bayan wani samame da dakarun runduna ta daya da rundunar Operation Whirl Punch suka kai a yankin Kampanin Doka, a ranar 1 ga Nuwamba, 2023, a kauyen Birnin Gwari na jihar Kaduna, wasu ‘yan bindiga hudu da suka addabi al’ummar yankin sun gamu da ajalinsu.

  • Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Sheikh Yusuf Ali 
  • Yadda Mahara Suka Kashe Mutane Da Sace Wasu Da Dama A Wurin Maulidi A Katsina

A yayin samamen, sojojin sun kwato bindiga kirar AK47 guda daya, kwalbasar harsashin AK47 daya da babura 14 da sauran kayayyaki daga hannun ’yan ta’addan.

A wani labarin makamancin haka, a samamen da rundunar ke kaiwa a yankunan Birnin Gwari ta jihar Kaduna, sojin sun samu nasarar kashe ‘yan bindigar har shida da kwato makamai a samame daban-daban.

Babban kwamandan runduna ta daya ta Nijeriya (GOC) wanda ke rike da mukamin kwamandan runduna ta Operation Whirl Punch, Manjo Janar VU Okoro, ya yabawa sojojin bisa jajircewar da suka yi, ya kuma umurce su da su ci gaba da kai samame har sai duk ‘yan ta’adda da masu aikata muggan laifuka a Yankin sun hadu da ajalinsu.

Labarai Masu Nasaba

Hako Man Fetur: Jihar Neja Ta Nemi Hadin Gwiwar Kamfanin Dangote

Aikin Ba Da Ilmi Ba Makamin Takarar Jam’iyyu Ba Ne

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Kaduna da su ci gaba da baiwa sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro bayanan tsaro masu inganci da za su taimaka wajen gano ayyukan ‘yan ta’addan da sauran masu aikata miyagun laifuka.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: KadunaSinSojoji
ShareTweetSendShare
Previous Post

IMF: GDPn Sin Zai Karu Da Kashi 5.4 A Shekarar 2023

Next Post

Darajar Cinikayyar Kasar Sin A Ketare Ya Karu Da Kaso 0.03% Cikin Watanni 10 Na Bana

Related

Hako Man Fetur: Jihar Neja Ta Nemi Hadin Gwiwar Kamfanin Dangote
Labarai

Hako Man Fetur: Jihar Neja Ta Nemi Hadin Gwiwar Kamfanin Dangote

11 minutes ago
Aikin Ba Da Ilmi Ba Makamin Takarar Jam’iyyu Ba Ne
Ra'ayi Riga

Aikin Ba Da Ilmi Ba Makamin Takarar Jam’iyyu Ba Ne

1 hour ago
Sojojin Sama Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴan Ta’adda, Ya Daƙile Hari Ranar Idi A Borno
Labarai

Sojojin Sama Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴan Ta’adda, Ya Daƙile Hari Ranar Idi A Borno

6 hours ago
Sojoji
Rahotonni

2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma

6 hours ago
Tufka Da Warwarar INEC Kan Yiwuwar Zaben 2023
Labarai

Ana Ci Gaba Da Samun Rudani Yayin Da INEC Ta Jinkirta Rajistar Sabbin Jam’iyyu

7 hours ago
Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya
Manyan Labarai

Dangote Ya Sanya Wa Hanya Sunan Tinubu, Zai Kashe Naira Biliyan 900 Don Gina Hanyoyi A Nijeriya

10 hours ago
Next Post
Darajar Cinikayyar Kasar Sin A Ketare Ya Karu Da Kaso 0.03% Cikin Watanni 10 Na Bana

Darajar Cinikayyar Kasar Sin A Ketare Ya Karu Da Kaso 0.03% Cikin Watanni 10 Na Bana

LABARAI MASU NASABA

Hako Man Fetur: Jihar Neja Ta Nemi Hadin Gwiwar Kamfanin Dangote

Hako Man Fetur: Jihar Neja Ta Nemi Hadin Gwiwar Kamfanin Dangote

June 7, 2025
Aikin Ba Da Ilmi Ba Makamin Takarar Jam’iyyu Ba Ne

Aikin Ba Da Ilmi Ba Makamin Takarar Jam’iyyu Ba Ne

June 7, 2025
Hukumar NPA Ta Bayar Da Kwangilar Aikin Ruwa Na Tashar Lekki

Hukumar NPA Ta Bayar Da Kwangilar Aikin Ruwa Na Tashar Lekki

June 7, 2025
Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya

Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya

June 7, 2025
Gwamnatin Tarayya Da Hadin Gwiwar IFAD Za Su Yi Wa Manoma Rijista Domin Tantance Su

Gwamnatin Tarayya Da Hadin Gwiwar IFAD Za Su Yi Wa Manoma Rijista Domin Tantance Su

June 7, 2025
Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin

Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin

June 7, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

June 7, 2025
Sojojin Sama Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴan Ta’adda, Ya Daƙile Hari Ranar Idi A Borno

Sojojin Sama Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴan Ta’adda, Ya Daƙile Hari Ranar Idi A Borno

June 7, 2025
Sojoji

2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma

June 7, 2025
Tottenham Ta Raba Gari Da Kocinta Ange Postecoglu

Tottenham Ta Raba Gari Da Kocinta Ange Postecoglu

June 7, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.