Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa kwanan nan ‘yan Nijeriya za su samu damar iya bibiya da sa ido kan ayyukan raya ƙasa waɗanda Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa.
Ministan ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja.
- Tinubu Ya Jajanta Wa Gwamnatin Canada Kan Gobarar Da Ta Tashi A Ofishin Jakadancinta
- An Fitar Da Gargadin Zubar Dusar Kankara Da Iskar Hunturu A Sassan Arewa Maso Gabashin Kasar Sin
A yayin ganawar, Idris ya ce, “Shugaban Ƙasa ya bada umarnin a yi amfani da fasahar zamani domin bai wa ‘yan Nijeriya damar sa ido, bibiya da bin diddigin ayyukan raya ƙasa waɗanda Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa a faɗin ƙasar nan.
Idris ya yi kira ga masu kafafen yaɗa labarai da su bayar da goyon baya kan wannan tsarin, ta hanyar buga sahihan labarai da yin adalci da sasaursu.
Ya ce, Gwamnatin Tarayya na ɗaukar dukkan sahihan labarai da muhimmanci domin amfanar ‘yan Nijeriya.
Ya Kara da cewa, gwamnatin Shugaba Tinubu za ta bada damar faɗar albarkacin baki ba tare da dannewa ko tauye haƙƙin kowa ba.
“Ku buga rahoton abin da ya tabbata, ku rabu da dukkan abin da ku ke shakku kan sahihancinsa.
“Wannan ƙasa tamu ce baki ɗaya, kuma haƙƙin dukkan ‘yan Nijeriya ne su taru su gina ƙasar. Kuma mun san Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ɗan gwagwarmayar dimokuraɗiyya ne.” Inji Ministan.
Idris ya ce Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na nan na fasalta gagarumin aikin wayar da kan ‘yan Nijeriya da za ta yi, ta yadda za a ƙara cusa wa jama’a kishi, ƙaunar ƙasa, haɗin kai da kuma kyawawan ɗabi’u.