A yayin bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin CIIE karo na shida da ake gudanarwa a birnin Shanghai, an baje sabbin kayayyaki masu dimbin yawa, kamar abin tsaftace kujerun zama a falo, da labulaye ba tare da cire su daga muhallin su ba, da na’urar zamani ta yin kwalliyar fuska, wadanda suke kunshe da manyan fasahohi kamar basirar dijital, da fasahohi marasa gurbata muhalli.
A yayin bikin CIIE na wannan karo, an kuma nuna sabbin kayayyaki, da fasahohi, da ma hidimomi har guda 442, wadanda aka fitar da su a karon farko. Kuma a bukukuwan CIIE da aka gudanar cikin shekaru 5 da suka wuce, an riga an fitar da sabbin kayayyaki, da fasahohi, da hidimomi har kusan 2000. To ko me ya sa aka fitar da sabbin kayayyaki a bikin na CIIE?
- Manzon Musamman Na Sin Kan Batun Yankin Gabas Ta Tsakiya Zai Halarci Taron Tallafin Jin Kai A Gaza
- Masu Kada Kuri’a: CIIE Na Kara Kuzari Kan Tattalin Arzikin Duniya
Amsar ita ce Sin tana da yawan al’umma fiye da biliyan 1.4, wadanda suka hada da masu samun matsakaitan kudin shiga fiye da miliyan 400, wanda hakan ya samar da wani babban wurin gwaji, da wurin fitar da sabbin fasahohi, da kayayyaki na kasa da kasa. Kayayyakin dake cike da basirar kirkire-kirkire, sun kyautata rayuwar al’umma, ta yadda suke cika bukatun masu saye-saye na Sin.
A sa’i daya kuma, yadda kasar Sin ta samu nasarar aiwatar da manyan tsare-tsaren raya kasa ta hanyar yin kirkire-kirkire, ya samar da damammaki ga ‘yan kasuwan waje wajen yin kirkire-kirkire. A watan Satumban bana, rahoton da kungiyar kiyaye ikon mallakar fasaha ta duniya ta bayar ya nuna cewa, Sin tana matsayi na 12 a duniya, kuma ita ce kasa daya tilo mai matsakaicin kudin shiga a cikin kasashe 30 na farko.
Har ila yau, ci gaban kasar Sin mai inganci yana ta jan hankalin duniya, Da yawa daga cikin masu halartar CIIE sun kafa cibiyoyin nazari a Sin.
Ana hasashen cewa, karin kamfanonin duniya za su zuba jari a Sin ta hanyar CIIE, inda ba oda, ko kasuwa, ko sabbin tunani kadai ba ne za su samu, har ma da damammakin da zamanintarwa irin na Sin ke kawowa. (Safiyah Ma)