Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta yi asarar sama da Naira tiriliyan 4.3 sakamakon satar danyen mai ta hanyar fasa bututai guda 7,143 a cikin shekaru biyar.
An bayyana wannan adadi ne a wajen taron fasaha da tsaro na kasa da kasa da aka gudanar a Abuja, inda aka bayyana irin illar da satar man fetur ke yi ga tattalin arzikin kasar nan.
- Shugaban Karamar Hukumar Lokoja, Muhammed Danasabe, Ya Rasu
- Gwamna Radda Ya Yi Allah Wadai Da Hare-haren ‘Yan Fashin Daji A Jihar Katsina
A wani jawabi da hukumar da ke tabbatar da cewa masana’antun da ke hako ma’adinai na aiki bisa gaskiya, (NEITI) ta gabatar a wajen taron, ta zayyana mummunan halin da ake ciki na satar man fetur,.
Shugaban NEITI, Ogbonnaya Orji, ya jaddada babbar illar satar danyen fetur, da illar da yake haifarwa wajen hako mai da cin hanci da rashawa da dakile bunkasar tattalin arziki da kasuwanci da kuma ribar kamfanonin mai.
Orji ya bayar da bayanai masu ban mamaki daga rahotannin NEITI, inda ya bayyana cewa a tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021, Nijeriya ta samu rahoton fasa bututun mai guda 7,143 da kuma fasa bututun mai da gangan.
Hakan ya yi sanadin satar ganga miliyan 208.639 na danyen mai da darajarsa ta kai dala miliyan 12.74 kwatankwacin Naira tiriliyan 4.325.
Kazalika Orji ya bayyana cewa, a cikin wannan lokaci, Nijeriya ta kashe zunzurutun kudi har Naira biliyan 471.493 don gyaran ko kula da bututan mai da suka lalace.