Mataimakin firaministan kasar Sin kuma jagoran tawagar kasar Sin a tattaunawar harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka Mista He Lifeng, ya gudanar da tattaunawa da dama da sakatariyar baitul malin Amurka Janet Yellen a birnin San Francisco na kasar Amurka.
He Lifemg ya je Amurka ne domin wata ziyara bisa gayyatar da bangaren Amurka ya yi masa.
- Xi Ya Ziyarci Kauyuka Domin Duba Rayuwar Manoma A Yanayin Sanyi
- CIIE Ta Bude Sabbin Damammaki Na Bunkasa Harkokin Cinikayya Tsakanin Sin Da Afirka
Bangarorin biyu sun yi kokarin aiwatar da muhimmiyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin jagororin kasashensu, don shirye-shiryen cimma sakamakon tattalin arziki a ganawar da shugabannin kasashen biyu za su yi a San Francisco, da dawo da dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu kan turbar da ta dace
Haka kuma bangarorin biyu sun yi musayar ra’ayi, kan dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, da yanayin tattalin arzikin kasashensu da ma duniya, da hanyoyin tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, da batutuwan dake shafarsu. (Ibrahim)