Sa’o’i kadan bayan Dokta Doyin Okupe ya mika takardar murabus dinsa a matsayin abokin takarar Mista Peter Obi na jam’iyyar Labour, Yusuf Datti Baba-Ahmed ya amince ya zama mataimakinsa.
Wata majiya cikin jam’iyyar ta bayyana cewa bayan tattaunawa mai zurfi a ranar Laraba, jam’iyyar ta amince da dan takarar mataimakin shugaban kasa na LP.
- Okupe Ya Janye A Matsayin Dan Takarar Mataimakin Jam’iyyar Labour Ta Peter Obi
- Maganar Hadewar Kwankwaso Da Peter Obi Ta Rushe
Za a bayyana Baba-Ahmed a hukumance a ranar Juma’a (gobe, 8 ga Yuli, 2022 a Abuja) don baiwa dan takarar shugaban kasa damar halarta bikin kaddamarwar a birnin tarayya Abuja.
Majiyar ta kuma bayyana cewa zabar tsohon Sanata, Yusuf Baba-Ahmed, a matsayin fitaccen dan gwagwarmayar yaki da cin hanci da rashawa, kuma sanannen masanin tattalin arziki, ya haifar da jin dadi a tsakanin magoya bayan Obi.
Tsohon Sanatan ya wakilci mazabar tarayya ta Zaria ta jihar Kaduna a daga 2003 zuwa 2007 kuma an zabe shi Sanata mai wakiltar Kaduna ta Arewa a shekarar 2011 a karkashin inuwar ANPP.
Shi ne wanda ya kafa Jami’ar Baze Abuja da Asibitin Jami’ar Baze wanda aka ce shi ne babban asibiti mai zaman kansa a Afirka a yau.
Batun zabar mataimaki na daga cikin dalilan da suka sa jam’iyyar Labour Party da NNPP suka kasa hadewa a matsayin Jam’iyya mai karfi ta uku a zabe mai zuwa, inda Rabiu Kwankwaso ya yi watsi da tayin.
Idan dai za a iya tunawa, a ‘yan kwanakin da suka gabata masu ruwa da tsaki na jam’iyyar LP sun tattauna da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Kwankwaso kan yadda za a kulla kawance gabanin zaben 2023 domin kayar da manyan jam’iyyun siyasa biyu – PDP da kuma jam’iyyar APC mai mulki.
Hakan dai ya kawo karshen cece-kuce a kan wanda ya kamata ya zama mataimakin.