Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; Zamantakewar aure, Rayuwar yau da kullum Rayuwar Matasa, Soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da matsalolin da ke afkuwa bayan raba gida da maigida ya yi, a yayin da ya ke yunkurin karo abokiyar zama (Kishiya), da kuma amfanin da ke tare da hakan.
Da yawan wasu matan na zabar raba gida a yayin da miji zai karo abokiyar zama, ta gefe guda kuma akan samu wadanda ba sa son a raba musu gida, wanda dalilin hakan ya sa shafin TASKIRA ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; Ko mene ne amfanin rabawar da kuma rashin rabawar? Wadanne irin matsaloli kowanne bangare zai iya haifarwa? Ta wacce hanya ya kamata a magance afkuwar hakan?Ga kuma ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Hafsat Sa’eed daga Jihar Neja:
Amfanin rabawa shi ne; samun saukin kishi. Rashin rabawa kuma yana kawo matsaloli da yawa musamman inba a shiri, amman in anbraba kowa da gidanshi kuwa, indai ba a sha’anin danginshi ko wata matsala ba babu me ganin juna sai dai in miji a tsaye yake a gidanshi, in kuwa an fi karfinshi a gida kuwa to inba bikin ‘family’ din miji ba babu inda za a hadu. Ina tunanin babu wata hanyar daya kamata a magance irin wannan matsalar face ta hanyar mijin, shi ne kadai zai iya magance matsalar gidanshi har in ba mijin hajiya bane shi. Shawara ga uwargida shi ne; tayi hakuri, namiji mijin mace hudune ba a haifa mata ita kadai ba, kila ma gidansu ba mamanta kadai ba, ita kuma amarya tabi uwargida koda ba gida daya suke ba, ina ganin shi ne zaman. Don kuwa babu wanda zai iya korar wani cikinsu, kuma kowa ana so aka aureta Allah ya sa mu dace ya rage mana zafin kishi.
Sunana Queen Nasmah daga Jihar Zamfara:
Amfanin raba kishiyoyi gida daya yana da matukar fa’ida, dan kowa ya ce zo mu zauna, to tabbas ya ce zo mu saba. Rashin hadewar yana da mahimmanci sosai wajen rage fada, kowa tana gidanta ba a hadu ba ballanta a yi fada, hadewar kuma yana da fa’ida wajen hada kawunan ‘ya’yan gida. Matsalar raba iyali na rage soyayyar ‘yan uwan juna, dan za su tashi babu shukuwa tsakaninsu, haka zalika hade su zai iya sa yaran su tashi babu jituwa tsakaninsu saboda yawan fadan da uwayensu mata suke yi, za a iya koya wa yaro makirci, kuma idan yara mata ne za su iya daukar dabi’ar iyayen nasu har gidan miji. Ina ganin rabawar ita ce hanya mafi sauki da za a samu zaman lafiya idan har mai gidan ya bi matakan da suka dace kamar haka; Lokaci bayan lokaci ya rika dauko yaransa yana kaiwa gidan daya, dan su saba , kuma su samu shakuwa a tsakaninsu, sannan kuma ya rika lura da masu shiga da fita cikin gidan saboda ma su tsegumi da kai gulma daga can zuwa can, ya kuma lura da kawayen da kowaccen su za ta yi mu’amala da su. Ni dai babbar shawarata da zan bada shi ne; su ji tsoron Allah, su guji fadawa halaka, yawan fada a gida babu abun da zai haifar musu, sai lalacewar tarbiyyar yaransu, wanda ku ke fadan nan saboda shi, ba soyayya ku ke nuna mishi ba , dan kuna jefa shi a fargabar tunkarar gida duk lokacin da ya dawo daga nema muku abunda za ku ci.
Sunana Sadik Abubakar Abdullahi, ‘Yammata, Rijiyar Lemo, Jihar Kano:
Kishi kumallon mata, in ji masu iya magana. Ba shakka wasu da dama daga cikin mata sukan zabi a raba musu gida da kishiyoyinsu, a cewarsu wai hakan ka iya zama hanyar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. A hujjojin da masu irin wannan ra’ayi suka rika akwai cewa; ba ma su hadu waje daya ba bare su ga abin da zai harzuka zukatansu har ta kaisu ga tashin hankali ko kuma nuna tsantsar kishin da yake kai mutum kogin nadama. Wasu kuma ko kadan ba su da ra’ayin a raba musu gidan, akan samu ittifaki daga bangaren uwargida da amaryar a kan suna son zama taren, ko ma mene ne zai faru sai dai ya faru, wai bera ya barar da garin mage. Masu irin wannan ra’ayi sukan nuna rashin yadda ga miji ne, a tunaninsu namiji zai iya fifita wacce ya fi so ta hanyar kulawa sosai tunda dayar ba za ta gani ba, don haka idan a tare suke kuwa bai isa ba. Raba gidan dai shi ne matsala domin tun asali shi Bahaushe zaman gandu ya gada, kuma zama ne mai dimbin alfanu. Matsalolin da raba wa mata gida kan haifar akwai; rashin jin dadin zamantakewar auren ga maigida, ba zai samu nutsuwa ba tunaninsa zai rabu biyu. Yaran da za a samu ba za su shaku da juna ba yadda ya kamata ba, bare har zumunci mai karfi ya kullu a tsakaninsu. Hakan nan idan maigida ba mai karfi ba ne kuma ba shi da wadatar muhallin kansa da zai raba wa matan, to tilas ya kama wa kowacce mata gidan da za ta zauna, a ƙarshe kuma zai fuskanci kalubalen biyan kudin haya. Hanyar magance wannan matsala ita ce hakuri da fahimtar juna tsakanin maigida da matansa, lallai ba a kara aure don cutar da uwargida ko kuma musguna mata. Hakan nan shi ma maigida ya yi kokarin kwatanta adalci a tsakanin iyalansa, sai su gamsu su zauna lafiya babu tashin-tashina.
Sunana Fatima Zara Alhassan (Ƴar mutan Argungu):
Amfanin raba gida yana kawo zaman lafiya a tsakanin mai gida (miji) da matansa, kuma mun san cewa zaman lafiya ai ya fi zama dan sarki. Rashin amfanin rabawa yana kawo rashin zaman lafiya musamman idan aka samu miji wanda ba ya adalci a tsakinin matansa, kun san kuma rashin zaman lafiya yana kawo tawaya ta komai na rayuwa. Raba gida yana da nashi matsalolin kamar haka; Rabuwar kan iyali, rashin zumunci. Rashin raba gida; Gurbacewar zumunta, rashin hadin kan matan gida, ganin laifin juna. Ni a ganina za a iya magance matsalar ta hanyar samun miji adali. Idan mai gida ya kasance mai adalci, to za a samu daidaito a tsakanin matayensa. Shawara ita ce; Su kasance tsintsiya madaurinki daya, su gani su ki gani. Su zauna lafiya a tsakaninsu, yin hakan zai kawo kwanciyar hankali a cikin gidansu, kuma yaransu za su tashi kansu a hade babu tashin hankali.
Sunana Aminu Adamu, Malam Madori Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya babu wani amfani muddun ba fada suke yi ba, domin hakan zai kawo rabuwar kai a tsakanin iyalai da rashin adalci a tsakanin matan, don haka raba gida muddun babu cikakken dalili bai dace ba. To magana ta gaskiya hakan yana kawo rabuwar kai a tsakanin iyalai da kuma rashin adalci a bangaren mai gida, domin iyaye mata za su ke kokarin raba kansu da kuma cusa tsana a tsakaninsu. To da farko dai ya kamata kai Maigida ka san matar da za ka aura, ma’ana kayi aure a gidan tarbiyya ta addini wanda ta san matsayin aure a musulunci da kuma muhimmancin kara auren, domin hakan zai taimaka ta fahimce ka lokacin da ka zo za ka kara auren ba za ta tada hankalinta ba, kuma ta taimaka wajen hada kan gidan. To ya kamata Amarya da Uwar gida su sani aure sunnah ce ta Manzon tsira Annabi Muhammad (S.A.W), don haka duk musulmin kwarai ba zai hana ayi ba, kuma idan har ba za a kara aure ba ‘ya ‘ya da suke haifa yaya za a yi da su?, don haka ya kamata su ji tsoron Allah, kuma su mazaje ya kamata su ji tsoron Allah su kyautatawa kowane bangare ba wai su zabi daya ba.
Sunana Hadiza Muhammad, Garin Gusau, Jihar Zamfara:
Amfanin rabawar a tawa fahimtar yana sanya nutsuwa ga matan, kasancewar kowacce bata ga abun da mijinta ya yi wa dayar ba. Rashin rabawar kuma na kara musu kusanci da juna tare da fahimtar juna, sannan ‘ya’yansu za su taso kansu hade. Babbar matsalar da rabawa ke haifarwa ga shi mijin, so-da yawa suna koyon rashin gaskiya. Saboda rashin ganin idon daya. gare su, matan kuma zargi na shiga. Matsalar rashin rabawar kuma ita ce; in ba a yi sa’a ba, aka samu rashin zaman lafiya a tsakanin matan, to ‘ya’yansu za su taso da irin akidarsu. Sai ya zama cewa an samu rarrabuwar kawuna. Hanyar daya kamata abi ita ce; da matan da mazan kowa ya ji tsoron Allah. A tsarkake zukata, sannan namiji yayi kokarin kwatanta adalci. Shawara anan ita ce maganar iyayenmu da kankaninmu, mu kyautata zamantakewarmu. Ke uwargida ki rike girmanki, amarya kuma ta sani ba wai dan miji baya son matarshi bane yake kara aure. Allah ya yi mana jagora, ya sa mu dace.
Sunana Yahaya Adam Aliyu, Dandishe Dala Jihar Kano:
To magana ta gaskiya raba musu gida ba shida amfani domin hakan zai kawo rabuwar kan ‘ya’yanyensu da kuma karancin shakuwa tsakanin iyalan baki daya. To gaskiya ya kamata maza kada su ce za su kara aure ba tare da tabbatar da adalci a tsakaninsu ba, sannan sai ka fara fahimtar da matarka faidar yin auren naka kafin kayi da amincewarta. To ya kamata a duk lokacin da namiji ya auri mata biyu ya yi kokarin tabbatar da adalci a tsakaninsu, babu bambanci tsakaninsu ko ‘ya’yansu, kuma mata su sani Manzon Allah (s a w) ne ya ce; Allah yana alfahari da Al’umma, mu yi aure dan mu hayyayyafa. To shawara ita ce su rungumi juna su zauna lafiya domin zama su biyu a gida samun saukin junansu ne ta fuskar taimakon junansu kamar rashin lafiya, haihuwa, abinci da sauransu.
Sunana Nabeela Dikko daga Jihar Kebbi:
A gaskiya raba muhalli wa mata abu ne mai kyau, amfaanin sa za a samu zaman lafiya, da mutunta juna sai kuma marmarin juna a tsakanin matan, domin duk abin da ido bai gani ba tsafta ce. Idan mata biyu ko fiye suna hade a wuri daya, ya kan haifar da hatsaniya da tashin hankali yau da gobe, amma kuma wani zubin idan suna raben akan samu zarge-zarge na an fi kyautatawa bangare daya, musamman idan uwargida na da ‘ya’ya ta kan za ci an fi kai wa amarya kayan dadi a gidanta. Hanya daya ce mata mu tsafta ce zukatanmu, maza a yi adalci a koda yaushe ko da matan na hade ko raben ku zama masu iya rike gidajenku. Shawara daya ce duk wacce ta iya allonta ta wanke, zancen ana tare gida daya ko ba a tare a ajiye a fuskanci kyautata wa miji a kuma zauna lafiya, sannan a guji kawayen banza a zauna zaman ibada domin Allah.