• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ziyarar Xi Ta APEC Na Nuni Da Kyakkyawar Sakamakon Yunkurin Daidata Dangantakar Sin Da Amurka

by CGTN Hausa
2 years ago
APEC

Bisa gayyatar da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron kolin kasashen Sin da Amurka, da taron shugabannin tattalin arzikin Asiya da Fasifik (APEC) karo na 30 da aka shirya gudanarwa a wannan mako a San Francisco. Kafin a kai ga wannan mataki mai nuni da murmurewar dangantakar kasashen biyu da ta yi tsami a cikin ’yan shekarun nan har ma ta kai ga “yakin mummuke”, bari mu waiwayi kadan daga cikin mu’amalolin baya-bayan nan da suka wakana tsakanin kasashen biyu kawo yanzu. 

Tun daga watan Yunin bana ne manyan jami’an Amurka da suka hada da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, da sakatariyar baitulmali Janet Yellen da sakatariyar kasuwanci Gina Raimondo suka ziyarci kasar Sin bi da bi. Bugu da kari, tattaunawar da aka yi tsakanin wakilin musamman na kasar Sin kan sauyin yanayi Xie Zhenhua da takwaransa na Amurka John Kerry a jihar California ta samu sakamako mai kyau. Daga bisani kasashen biyu sun kafa kungiyoyin harkar tattalin arziki da na kudi da sauran hanyoyin musaya da hada-hadar kudi da cinikayya.

  • Firaministan Pakistan Kakar: Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Tana Girmama Bambance-bambance A Tsakanin Kasa Da Kasa
  • Yawan Kayayyaki Da Aka Yi Jigilarsu Na Kasar Sin Ya Kai Matsayi Mafi Girma A Bikin Sayayya Ta “Double 11” 

A karshen watan Oktoba kuma, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai ziyara kasar Amurka, inda ya gana da Biden, ya kuma tattauna da wasu manyan jami’an siyasa, da masu ruwa da tsaki da ’yan kasuwa na Amurka. Kazalika, He Lifeng, mataimakin firaministan gwamnatin kasar Sin, kana shugaban kwamitin harkokin tattalin arziki da kasuwancin Sin da Amurka na kasar Sin, shi ma ya ziyarci Amurka daga ranar 8 zuwa 12 ga wannan watan Nuwamba.

A karon farko, Amurka ta aika da wata babbar tawaga zuwa bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na shida (CIIE) da aka kammala a Juma’ar makon jiya. Ana ci gaba da yin mu’amala mai zurfi, kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta nuna alamun murmurewa.

Ginshikin alakar Sin da Amurka na dogaro ne da mu’amala tsakanin al’umman kasashen biyu. Kama daga ’yan kasuwan Amurka dake ziyara a kasar Sin, zuwa shirin “Bond with Guling: dandalin sada zumunta tsakanin Sin da Amurka na shekarar 2023,” da kuma tawagar wakilan Flying Tigers na Amurka da suka ziyarci kasar Sin, duka wadannan mu’amaloli sun nuna kyakkyawar fahimta da zurfafa zumunci, wanda hakan ya kara karfafa zumunci da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

LABARAI MASU NASABA

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Ana sa ran halartar shugaba Xi a taron kolin Sin da Amurka da taron kolin kungiyar APEC zai tabbatar da fahimtar ci gaban kasar Sin dake dauke da tarihi mai muhimmanci, da taimakawa kasashen duniya samun karin wadanda za su jagoranci ci gaban duniya ta hanyar yin amfani da tsarin zamanantarwa irin ta kasar Sin.

A gun taron kungiyar APEC da za a yi, kasar Sin za ta ci gaba da daukar nauyin da ya rataya a wuyanta a matsayinta na babbar kasa, da kokarin tabbatar da cewa kasuwanni masu tasowa da kasashe masu tasowa sun fi samun wakilci, da damar bayyana ra’ayoyinsu a harkokin duniya, da kuma sa kaimi ga ci gaba da kyautata tsarin mulkin duniya. (Muhammed Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu
Daga Birnin Sin

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Next Post
Ganawar Da Shugabannin Sin Da Amurka Za Su Yi Za Ta Iya Amfanin Duniya

Ganawar Da Shugabannin Sin Da Amurka Za Su Yi Za Ta Iya Amfanin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

November 6, 2025
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa A Sakkwato

November 6, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025

November 6, 2025
Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025
Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.