A ranar 15 ga watan Nuwamba, bisa agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Amurka, Joe Biden, a wani wurin da ake kira Filoli a birnin San Francisco na kasar Amurka.
Xi ya ce, yanzu shekara daya ta wuce, tun bayan ganawarsa da Biden a tsibirin Bali. Kuma a shekara daya da ta gabata, abubuwa da dama sun wakana. Duniya ta samo mafita daga yaduwar cutar mashako ta COVID-19, amma har yanzu annobar na haifar da babban tasiri. Kana, tattalin arzikin duniya ya fara murmurewa, amma ba shi da karfi sosai, al’amarin da ya kawo tsaiko ga tsarin sana’o’i, da tsarin samar da kayayyaki, kuma ra’ayin bada kariya ga harkokin cinikayya na kara tsananta. A matsayinta na alakar bangarori biyu mafi muhimmanci a duniya, kamata ya yi a yi la’akari, gami da tsara shirin raya dangantakar Sin da Amurka daidai bisa yanayin da ake ciki yanzu, wato gaggauta samun sauye-sauye a duniya, ta yadda za’a samar da alfanu ga al’ummomin kasashen biyu, da zama abun misali ga ci gaban harkokin dan Adam.
- Sinawa Masana Kimiyya Sama Da 1,200 Ne Suka Shiga Cikin Jerin Masu Bincike Da Aka Fi Amfani Da Ayyukansu A Duniya
- Shugaba Xi Ya Isa Birnin San Francisco Don Ganawa Da Takwaransa Na Amurka Da Halartar Taron Shugabannin Mambobin Kungiyar APEC
Shugaba Xi ya kara da cewa, cikin sama da shekaru 50 da suka gabata, dangantakar Sin da Amurka ta sha fuskantar matsaloli iri-iri. Duk da cewa akwai sabani, amma tana samun ci gaba. Ba zai yiwu irin wadannan manyan kasashe biyu su zamo ba sa mu’amala da juna ba. Kana, duk wani yunkuri na wani bangare na sauya dayan bangaren, ba zai ci nasara ba, kuma babu wani bangaren da zai iya jure sakamakon rikicinsu.
Ya ce, har yanzu ina da imanin cewa, takara tsakanin manyan kasashe masu karfin fada a ji ba ita ce taken wannan zamani ba, kuma ba za ta warware matsalolin Sin da na Amurka da na duniya baki daya ba. Wannan duniya na da fadin da zai wadatar da Sin da Amurka, kuma nasarorin mu damammaki ne gare mu baki daya. Banbancin tarihi, da al’adu, da tsarin zamantakewa, da turbar ci gaban Sin da Amurka al’amura ne na zahiri. Ko shakka ba bu, muddin bangarorin biyu sun rungumi akidun mutunta juna, da zaman jituwa, da hadin gwiwar cimma moriya tare, za su iya shawo kan daukacin banbance banbance, tare da lalubo hanya mafi dacewa ta zaman jituwa tsakanin wadannan kasashe biyu masu karfi a duniya. Ina da yakinin cewa, alakar Sin da Amurka na da kyakkyawar makoma.
Ya ce, ni da shugaban kasa, muna jagorantar alakar Sin da Amurka, muna dauke da nauyin al’ummun mu, da duniya, da tarihi. A yau ina fatan zurfafa musayar ra’ayoyi tare da shugaban kasa, kan batutuwan da suka jibanci alakar Sin da Amurka, da ma manyan batutuwan da suka shafi wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya, tare da cimma sabon daidaito. (Murtala Zhang, Saminu Alhassan)