Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya gabatar da kasafin kudi na naira biliyan N298.14 a matsayin kasafin kudin jihar na shekarar 2024.
Gwamnan ya tsara kasafin ne bisa ajandarsa mai dauke da abubuwa 12 da ya tanada domin samar da ci gaba a jihar.
- Yadda Wani Saurayi Da Budurwa Suka Daura Wa Kansu Aure A Jigawa
- Kungiyar Kwadago Ta Janye Daga Yajin Aikin Da Ta Shiga
Gwamna Namadi ya gabatar da kudirin Naira biliyan N111.98 wanda ke wakiltar kashi 37 cikin 100 na kasafin kudin don ci gaba da ayyukan yau da kullum da kuma naira biliyan N175.44 wanda ke wakiltar kashi 59 cikin 100 don gudanar da ayyukan kasa a jihar.
Bangaren ilimi ya dauki kaso mafi tsoka na biliyan N95.5, inda aka mayar da hankali wajen daukar malamai aiki, da inganta sana’o’in hannu, da mayar da yaran da ba su zuwa makaranta ajujuwa, da kuma kafa hukumar Tsangaya don sake fasalin tsarin Almajirici cikin tsarin ilmantarwa na zamani.
Bangaren kimiyya da sadarwa (IT) ya samu kasafin kudi a karon farko wanda ya kai Naira biliyan N1.23 da kuma Naira biliyan 4.4 don karfafa matasa da mata.
Gwamnan ya bukaci majalisar dokokin jihar da ta gaggauta duba kasafin kudin domin baiwa gwamnatinsa damar gudanar da ayyuka domin more romon dimokuradiyya a jihar.
A nasa bangaren, kakakin majalisar dokokin jihar, Honarabul Haruna Aliyu Dangyatin ya yi alkawarin tabbatar da amincewa da kasafin kudin kafin sati na Uki na cikin watan Disamba.
Ya yabawa gwamnan jihar, Malam Umar Namadi bisa gabatar da kasafin kudinsa na farko wanda a cewarsa, kyawawan manufar gwamnan na hangen nesa na ganin ci gaban Jihar Jigawa ya fito a fili karara.