Akalla wasu ‘yan gudun hijira uku ne suka rasu sannan sama da gidaje 1000 suka kone bayan da gobara ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Alamdari da ke Maiduguri a Jihar Borno.
Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 6 na safiyar Laraba kuma ta dauki sama da awa daya kafin jami’an kashe gobara su shawo kan ta.
- Mun Yarda Mu Hada Kai Da Atiku In Zai Marawa Kwankwaso Baya A 2027 – NNPP
- Gwamnan Jigawa Ya Gabatar Da Kasafin Naira Biliyan N298.14bn Na Shekarar 2024
Babban Darakta Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar, Dokta Barkindo Muhammad Sa’idu ne, ya bayyana hakan a Maiduguri ga manema labarai.
Ya ce jami’an sa-kai na CJTF, da jami’an tsaro da ‘yan gudun hijira, sun taimaka wajen kashe gobarar.
An samu asarar dukiya a sanadin tashin gobarar.
Tuni dai gwamnan Jihar, Babagana Umara Zulum ya kafa kwamiti don gudanar da binciken musababbin tashin gobarar.