Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi ya bayyana yadda babban bankin Nijeriya (CBN) ya karya darajar naira.
Sanusi ya bayyana cewa, ba da lamuni da CBN ya bai wa gwamnatin tarayya karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta hanyoyi daban-daban, ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya, wanda ya kai ga faduwar darajar naira.
- Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC
- Da Ɗumi-ɗuminsa: EFCC Ta Gabatar Da Tsohon Gwamnan CBN A Gaban Kotu
Ya bayyana hakan ne da yake jawabi a wurin taron kasuwanci na MTN a ranar Talata. Sanusi ya yi nuni da cewa, CBN ya tsunduma cikin matsananciyar karancin kudade ta hanyar amfani da wasu matakai daban-daban, da suka hada da bude kasuwannin harkokin kudade, da OBB da kuma haraji.
Ya bayyana cewa, wadannan matakan sun nuna yadda babban bankin ya jajirce wajen gudanar da ayyukansa na tabbatar da daidaiton tsarin hada-hadar kudi da kuma shawo kan hauhawar farashin kayayyaki.
“Ina da kyakkyawan fata, musamman a cikin gajeren lokaci abubuwa za su daidaita. Mun sami shekara takwas ba tare da daidaita abubuwa ba a babban bankin Nijeriya.
“Hakan ya kara habaka hauhawar farashin kayayyaki da kuma raunata darajar naira, wannan shi ne gaskiyar lamari.,” in ji shi.