Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da kwangilar gyaran na’urorin samar da wutar lantarki na layin watsa wutar lantarki mai karfin 330kV da 132KV dake bangaren tekun Legas a kan kudi dala 968,818.
Ministan Wutar Lantarki, Abubakar Aliyu, ya ce abin da ke cikin kwangilar a bakin teku a tsohon lissafi ya kai N7.393m.
Kamfanin da ya samu kwangilar shine Rab Power Industries Limited.
Ya ce: “Kwangilar gyaran ta hada da tashar Iantarki da ke Katsina da kuma tara a Kano, kamar yadda Aka sani, wata tashar wutar lantarkin tana cikin teku wata kuma a wajensa.
“Don haka, wannan gyaran ya shafi tashoshin bangaren bakin teku ne kawai. Kuma kudin ya kai N445,326,643.12. Da ana bjyan kudi Naira Miliyan N939,410,664 a bakin teku amma yanzu ya koma Naira Miliyan N1,938,737,307.12 kuma majalisar ta amince da hakan.”