A halin yanzu kallo ya koma sabon babin da aka bude na kyautata alaka a tsakanin giwayen kasashen duniya biyu, Sin da Amurka yayin da aka yi ganawar keke-da-keke a tsakanin Shugaba Xi Jinping da takwaransa Joe Biden a birnin San Francisco na Amurka, ranar Laraba.
Bayan ganawar, shugabannin biyu sun jaddada muhimmancin dake akwai na dukkan kasashen duniya su mutunta juna da kuma samar da hanyar zama cikin lumana da barin kofofin sadarwa a bude tare da dakile rikici.
- Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi Yayin Kwarya-kwaryar Taron Shugabannin APEC
- Wakilan Sin Da Kenya Sun Halarci Dandalin Tattaunawa Kan Hanyoyin Zamanintar Da Kasa
Sun amince da karfafa tattaunawa da hadin gwiwa a bangarori daban-daban, ciki har da kafa wata gamayya da za ta yi aiki kan yaki da muggan kwayoyi, da maido da manyan hanyoyin sadarwa na soja da kuma tinkarar matsalar sauyin yanayi tare.
Kamar yadda shugaban cibiyar bincike kan al’amuran kasar Sin ta 22V Research, Michael Hirson ya fada, ganawar shugabannin biyu za ta zama rigakafin magance rikicin da babu wanda yake da muradin gani a tsakaninsu.
Sabanin Amurka da Sin ya karu a shekarun baya musamman a karkashin gwamnatin Trump sakamakon kare-karen haraji da kuma takunkuman fasaha a karkashin gwamnatin Biden.
Sai dai alaka ta fara kyautatuwa bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya kai wata ziyara a birnin Beijing a watan Yuni, kana a farkon watan Oktoba, shugaban masu rinjaye na majalisar dattijan Amurka Chuck Schumer da wasu ’yan majalisar dattawan Amurka biyar dake wakiltar jam’iyyun Republican da Democrat, sun yi wata ganawa ta mintuna 80 da shugaba Xi Jinping.
“Dangantakar da ake gani a halin yanzu tsakanin Sin da Amurka ta sa duniya ta numfasa”, a cewar Shen Yamei, daraktan sashen nazarin Amurka, kuma abokiyar bincike a cibiyar nazarin kasa da kasa ta kasar Sin.
Kamar yadda Shugaba Xi ya sha nanatawa a baya kuma ya sake jaddada a yanzu, gasa mara tsafta a tsakanin manyan kasashen duniya ba ita ake yayi ba a wannan zamanin, a cewarsa, duniya tana da fadin da manyan kasashen biyu za su sakata su wahala cikin nasara. Don haka samun nasarar kowace kasa a tsakaninsu, wata dama ce ta ci gaba ga ’yar ’uwarta.
Abin sha’awa da kuma ke nuna shugabannin biyu sun hau turba guda, shi ma shugaba Biden ya sha alwashin cewa ba zai mayar da gasa a tsakanin kasashen biyu ta zama ta rikici ba, ya kuma yi kira da a yi kokarin hadin gwiwa don tunkarar kalubalen duniya.
Wani abu dake kara nuna cewa Sinawa da Amurkawa na da kyakkyawar fatan cin moriyar juna shi ne, yadda sama da masu baje kolin Amurka 200 daga bangaren noma, na’urori masu sarrafa kwamfuta, na’urorin likitanci, motocin zamani masu aiki da sabbbin makamashi, kayan kwalliya, da dai sauransu suka halarci bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su na kasar Sin karo na shida (CIIE) da aka kammala kwanan nan a Shanghai. Ba a taba samun Amurkawa masu yawa da suka halarci bikin kamar a bana ba a tarihin bikin baje kolin.
A cewar bankin duniya, Amurka tana da karfin hada-hadar tattalin arziki na GDP na a kalla tiriliyan 25.5 a bara, yayin da na Sin ya kai kusan dala tiriliyan 17.9, wanda ya kai sama da kashi uku na tattalin arzikin duniya idan aka hade. Kasar Sin da Amurka suna da kusan kashi daya bisa hudu na al’ummar duniya, kuma cinikin da ke tsakanin kasashen biyu ya kai kusan kashi biyar na jimillar na duniya kaf.
Ba Amurka da Sin kawai idan dangantaka mai gwabi ta dore a tsakaninsu zai amfanar ba har da sauran kasashen duniya, kasancewar hakan za ta kara bude sabbin hanyoyin cinikayya musamman ganin cewa kasashen biyu ke da kashi daya bisa hudun yawan al’ummar duniya.
Kamar yadda Shugaba Xi ya bayyana a jawabinsa na bude taron kasashen biyu a ranar Laraba, “akwai bukatar manyan kasashen su rika nuna cewa su manya ne a aikace” saboda hakan na da matukar muhimmanci ga samar da ci gaban duniya cikin hanzari da ba a ga irinsa ba cikin karni.
Muna fata zumunci ya dore tare da kauce wa komawa ’yar gidan jiya.( Abdulrazaq Yahuza)