Usman Baba Pategi, wanda aka fi sani da Samanja Mazan Fama an haife shi ne a ranar 20 ga Mayu shekarar 1942, sojan Nijeriya ne mai ritaya, ya rasu ranar 12/11/2023.
Bayan barin aikin soja, Pategi tare da Yusuf Ladan da Mamman Ladan da Idi Jibril maaikatan NTA sun gabatar da wani shirin barkwanci na Hausa da aka fi sani da fina-finan Arewacin Nijeriya ko fina-finan Hausa a shekarun 1980 ga masu kallon tashar gidan talabijin na Radio Kaduna.
- Allah Ya Yi Wa Fitaccen Tsohon Dan Wasan Hausa, Usman Baba (Samanja) Rasuwa
- Mun Sha Duka Da Zagi A Hankoron Kawo Ci Gaba A Kannywood -Chiroki
Samanja Mazan Fama dan gidan sarautar Pategi ne a Jihar Kwara da ke Arewa ta tsakiyar Nijeriya, Pategi da ne ga Etsu Usman Patako marigayi Sarkin Pategi.
Ya fara karatunsa na farko a makarantar firamare ta Pategi sannan ya tafi makarantar Middle School ta Ilorin, daga baya ya tafi Kaduna ya zauna da kawunsa Alhaji Audu Bida wanda ya zama yana yi masa wasu aikace aikacen gida.
Ya kuma yi aiki a wani kantin sayar da kayan aikin injiniya, kafin ya fara aiki da tashar watsa labarai na arewacin Nijeriya (Northern Broadcasting Corporation, (NBC) a Kaduna.
Ya shiga aikin sojan Nijeriya a shekarar 1960 inda wani kaftin din Soja a lokacin yakin basasar Nijeriya ya zo neman matasa a Arewacin Nijeriya don su shiga aikin Soja.
Daga nan ne Pategi ya bar aikin yada labarai ya shiga aikin soja, ya samu horo a makarantar horar da sojoji ta Apapa, ya yi aiki a karkashin Janar Sani Abacha da Janar Sani Sami.
Daga baya ya yi ritaya a shekarar 1985, ya ci gaba da aikin wasan kwaikwayo a FRCN Kaduna, ayyukansa a wancan lokacin sun hada da bayar da umarni da rubuta fina-finai, galibi ana kiransa da Samanja Mazan Fama, ma’ana Sajan-Major saboda kwarewar da ya samu a aikin soja.
A shekarar 2010, ya je kasar Indiya domin jinyar ciwon zuciya wanda daga baya shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ba shi Naira miliyan 1.5, kamar yadda gidan rediyon tarayyar Nijeriya FRCN ya ruwaito.
An haifi Pategi a babban gidan sarauta, wanda babansa shine Mai Martaba Etsu Pategi na wancan lokacin, amma duk da cewar shi jinin sarauta ne,
Samanja ya gwammace da ya ci gaba da aikinsa na wasan kwaikwayo a gidajen talabijin ba tare da ya waiwayi kujerar sarautar gidansu ba, duk da cewar kuma shi ne magajin masarautar Etsu Pategi.
Bayan rasuwar mahaifinsa Sarkin Pategi Etsu Usman Patako, Samanja ya ki yarda ya zama sabon sarkin Pategi a wancan lokacin, ya bar sarautar ga kaninsa Etsu Umaru Chatta wanda ya rasu a shekarar 2017 kuma Umaru Bologi ya gaje shi.
Galibi Pategi yakan bayyana a matsayin dan sanda ko soja a cikin wasannin kwaikwayon da yakan fito, da aka tambaye shi dalili, Samanja ya bayyana cewar yafi sha’awar ya fito a wannan matsayin domin duk da cewa ya bar gidan Soja, amma har yanzu yana jin aikin a jikinsa a duk lokacin da ya saka kakin Soja.
Ya samu sunan Samanja ne domin kwaikwayon sunan mukamin Soji na Sajan Manjo, kuma ya bayyana cewa yin wasan kwaikwayo yana kara masa farin ciki shi ya sa ya yi ritaya daga aikin Soja ya koma aikinsa na wasan kwaikwayo.
Daga cikin shahararrun wasannin da Samanja ya fito kuma suka yi tasiri a masana’antar wasan kwaikwayo ta Hausa akwai Samanja, Yusuf Ladan, Zaman Duniya Iyawa Ne da sauransu.
Pategi ya shahara a fim din Samanja duba da yadda yake hada kalmomin Hausa/English da pidgin a cikin maganganunsa kamar yadda sojojin Nijeriya ke magana.
Baba Pategi ya rasu ya bar mata uku da yaya 20, ya rasa daya daga cikin matarsa Hajiya Maryam Baba tana da shekara 46 a duniya.