Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hada da; Zamantakewar Aure, Rayuwar yau da kullum, Rayuwar Matasa, Soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin kalubalen da wasu ‘yan matan ke fuskanta a wajen samarinsu, yayin da saurayi zai shafe tsawon mako daya ko biyu ba tare da ya nuna kulawa ga masoyiyar tasa ba, bare ya yi mata magana ko da kuwa sun ci karo da juna a ‘online’, har sai lokacin da ya yi ra’ayin kula ta, yana jira ne kawai ita ta rinka kiransa ko ta rinka nemansa tana kula shi. Yayin da wani daban ya kai kudin aurenta kuwa ya rinka masifa tare da bakaken maganganun cewa; ta yaudare shi, ta ci amanarsa, yana son ta ta guje shi, da dai sauran munanan kalamai.
‘Yan matan da hakan ke faruwa gare su sukan rasa gane irin wannan dabi’ar, shin soyayya ce ko kuma rainin wayo? Dalilin hakan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; Ko wa ya dace ya rinka yawan kiran wani a waya da yawan ba da kulawa tsakanin saurayi da budurwa? Wadanne hanyoyi ya kamata wanda yake son mace ya rinka bi?
Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Queen Nasmah daga Jihar Zamfara:
Gaskiya a tawa fahimtar babu babban raini wayo kamar wannan, ita fa kowace rayuwa babu abun da take bukata sama da kulawa, wanda yake sonka duk rintse ba zai rasa lokacin da zai duba ka ya ga ya lafiyarka take ba, ban san yadda saurayi zai shafe sati biyu ko daya bai nemi ni ba, kuma na saka shi a jerin masoya. Gaskiya dai ko yana son nata toh soyayyar ragagga ce, bata kai kuloluwar yadda zai kula ta ba, in dai ni ce toh zan ce mata ki nemi wanda zai kula da ke, dan tun a waje zai iya watsar da ke har na tsawon lokaci ina ga an yi aure an zama daya. Namiji shi ne yake da kaso sittin cikin dari na kiran waya, idan har ya gaza da hakan to tabbas soyayyar ta samu rauni. Idan har kana son mace, to duk yadda take sonka ka dage da kulawa da ita, kyautata mata da kuma bata shawara,.ina mai tabbatar maka da wuya a kasa ka, idan ka rike wadannan matakan idan ko har ka gaza, wani ya zo yana mata hakan to tabbas za ka rasa. Gaskiya babu wata shawara da zan ba su, dan shi hali zanen dutse ne, ko sun fara sai sun daina, amma dai ke mace idan ki ka ga mai irin wannan hali idan har baya da kwakkwaran dalili kawai ki canza shi, ina ga idan suka ga ana kyale su za su dawo hankalinsu.
Sunana Aminu Adamu, Malam Madori Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya wasu mazan ayyuka suke musu yawa har su hana su sukunin da za su samu damar kiran waya, wasu kuma tana iya yiyuwa rainin wayo ne, to amma kuma ai idan da so ba maganar rainin wayo. To maganar akai-akai namiji ya dace ya rika kira akai-akai, to amma ba laifi ba ne don mace ta kira jifa-jifa, domin yana nuna ita ma ta damu da shi, ba wai shi kadai ya damu da ita ba. To akwai bukatar dai a gina tubalin soyayyar a bisa gaskiya da rikon amana da kuma tabbatar da kaunar juna, domin shi ne zai taimaka wajen yin soyayya ta gaskiya da za ta taimaka aje ga aure. To da farko dai ya kamata su sani soyayya bata yin karko idan ba a mutunta juna, domin ganin mutuncin juna shi ne jigo na soyayya ta hakika dake kaiwa ga aure, kuma samu zaman takewa dadi, don haka mutunta juna yana dadi a soyayya.
Sunana Hadiza Muhammad, daga Gusau Jihar Zamfara:
Rashin kiran waya wasu lokutan nada alaka da yanayin rayuwar mutum. Gaskiya wannan rainin wayo ne, wadda ka ke so ba za ka iya shareta wani tsawon lokaci, ba tare da ka kula da ita ba. Da namiji da mace, kowa ya dace ya kira dan’uwa ya ji ya yake, kowa nada hakkin samun kulawa ga abokin soyayya. Hanyoyin daya kamata su ne; ya sauke duk wani nauyi na soyayya daya rataya a wuyanshi. Shawarar da zan ba maza masu irin wannan dabi’ar shi ne; su daina. Su rinka kiran ‘yan matansu dan jin lafiyarsu, da kuma fada musu dadadan kalamai, in ba haka ba, a cikin sauki za a iya kwace musu budurwa. Allah Ya kara daukaka jaridar LEADERSHIP tare da shafin TASKIRA.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Jihar Kano, Karamar Hukumar Rano:
Wannan ai ba dabi’ar masoyin gaskiya bace, duba da an san namiji da iya ririta da bawa mace kulawa a soyayya, ya kamata dai a wajen nema namiji yana yawan kula da mace idan kuma aka yi aure wannan kuma ya koma kan ita macen. Kowa ya dace yana kiran kowa amma sai a duba yanayi na rayuwa, domin wallahi yanzu wasu matan sun fi samarin lokaci, amma ban ware daya ba sai dai kawai a al’adar malam bahaushe to wannan ya rataya ne akan namiji. Yana bata lokaci koda na awa 1 ko 2 a rana idanma akwai lokaci ya fi haka, domin indai har ana son juna to yin hakan yana taka muhimmiyar rawa ko a wajen zaman aure ne.Su canja tunani domin mace mai rauni ce kuma rashin bata lokacinka ko ya ya yake sa ta sami wani wanda yake bata lokacin dole wata rana “KAJI KIDA A MAGWAN” wanda ba hakan ake fata ba.
Sunana Fatima Yusuf Ibrahim, Gama-D Layin Mai Unguwa Nasiru:
Wannan rainin wayo ne ba soyayya ba, saboda da yana santa ba zai yu ya ga tana catin ba ya ce wai sai ya jira ta masa magana ba, da yana santa tuni ma zai mata magana har in bata bashi amsa ba ya ji haushi. Shawara shi ne ya kamata ya dinga kiranta yana bata kulawa ta musamman, amma ita ma ya kamata ta dinga kulawa da shi, sabida ko shuka ce idan baka bata ruwa bushewa take. Hanyar da ya kamata yabi ita ce; ya zama me kulawa da ita ya gane mene ne take so da wanda bata so, hakan zai sa ta so shi ko bata son shi. Shawarar ita ce; su daina saboda hakan zai iya janyo musu damuwa a rayuwar su, Allah ya jarabbce shi da matsananci san ta, kuma wani ya riga ya kai kudi babu yadda mutum zai yi sai da-na-sa-ni a rayuwarsa.
Sunana Umar Adamu, Malam Madori Jihar Jigawa:
Tabbas hakan yana nuna ba a mutunta juna, ita soyayya bata dorewa muddun ba a mutunta juna, to amma batun rashin kira akai-akai tana iya yuwa ayyuka ne suka yi masa yawa, amma wasu kuma rainin wayo ne. Eh maganar kira namiji ne ya dace ya rika kira akai-akai domin hakan zai nuna ya damu da ita kuma yana bata kulawa, domin soyayya ba ta dorewa idan babu kulawa, to amma ba laifi ba ne idan macen tana kira lokaci zuwa lokaci. To magana ta farko dai a gina soyayya akan gaskiya da rikon amana, domin hakan zai taimaka wajen yin soyayya tsakani da Allah da kuma mutunta juna da tausayawa juna ko bayan aure. Shawara ita ce; a mutunta juna domin mutunta juna shi ne ginshikin gina soyayya ta gaskiya wadda ta kai ga auren soyayya da mutunta juna da tausayawa juna har abada.
Sunana Zainab Zeey Ilyasu daga Jihar Kaduna:
A gaskiya wannan rainin wayo ne, kuma ba sonta yake yi ba, domin da yana sonta ba zai taba kallonta a online ya ki kula ta ba, ko kuma ya zauna jiran sai lokacin da ta kula shi. Ai a al’adar Malam Bahaushe mace ba ita ce ya kamata ta fi bawa namiji kulawa ba muddin ba a yi aure ba, shi namijin shi ya kamata ya bawa mace kulawa, kiranka ya fi nata yawa, nemanka ya fi nata yawa, ba wai ka zauna ka shafe tsawon sati babu ko kala kuma kana can kana catin da wata kna kallonta, sai ranar da abokiyar hirarka bata nan sannan za ka samu damar kula ta, kuma wai a haka soyayya ce ko na ce sonta ka ke, ai ka yaudari kanka wallahi. Ni idan ni ce ma ‘blocking’ dinsa zan yi dan ba shi da wani amfani a wajena, yawan kulawarka ga mace, yawan yadda ita ma mace za ta baka kulawa, amma ka sani dole ne yawan kulawar namiji ya fi na mace tunda su mata da kunya aka san su. Ko kai kanka ka ga mace kullum baka kula ta ita take nemoka tana kulawa ai ka ji sam! ba ta yi maka ba, kamar mara kamun kai, za ka ji yadda take maka haka take yi wa sauran maza, amma in kai ne daman namiji aka fi sani da jure yawan kulawa ga mace.
Sunana Musbahu Muhammad Gorondutse Jihar Kano:
Sakaci da rashin kulawa ne hakan. Namiji ne ya kamata saboda shi ne yake fita nema ita kuwa Mace ai a gida aka santa. Ya kamata a dinga bawa Mace kulawa da kalamai masu dadi da sanyi. Namiji ya kamata ya dinga bawa soyayyarsa kulawa kamar kyautatawa, kulawa da nuna kauna sosai ga macen da yake so.