Daga ranar 14 zuwa 17 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi wata ganawa ta musamman da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden, tare da halartar kwarya-kwaryar taron kolin shugabannin kungiyar hadin kan tattalin arzikin yankin Asiya da tekun Pasifik karo na 30, bisa gayyatar da aka yi masa.
Shugaba Xi yana da abokai da yawa a kasar Amurka. A yayin liyafar maraba da kungiyoyin fararen hula abokan kawancen Amurka suka shirya, Xi ya ce jama’a ne suka rubuta labarin hadin gwiwar kasashen Sin da Amurka.
- Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi Yayin Kwarya-kwaryar Taron Shugabannin APEC
- Gimbiya Sirindhorn Ta Thailand:Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Inganta Hadin Gwiwar Al’ummun Kasa Da Kasa
Bayan samun labarin cewa, shugaba Xi Jinping ya isa kasar Amurka, sai daliban makarantar sakandaren Lincoln dake Tacoma na birnin Washington D.C., suka gabatar da wani zane da suka tsara a matsayin kyauta ga shugaban kasar Sin Xi Jinping da mai dakinsa Peng Liyuan. Da wannan kyauta, malamai da daliban makarantar sakandaren Lincoln, sun bayyana dadaddiyar abota da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, da kuma fatansu na samun kyakkyawar makoma a tsakanin kasashen biyu.
A yayin ziyarar da ya kai kasar Amurka, Xi ya bayyana shirin fadada mu’amala tsakanin al’ummomin Sin da Amurka, musamman ta hanyar tattaunawa tsakanin matasa. Ya ce, nan da shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin na son gayyatar Amurkawa matasa dubu 50 da su zo kasar Sin domin yin musanya da kuma karatu. (Ibrahim)