Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben gwamna Caleb Muftwang na jihar Filato.
Wani kwamiti mai mutane 3, a wani mataki da ya yanke a ranar Lahadi, ya ce Muftwang ba cikakken dan jam’iyyar PDP ba ne.
- Halin Maza Muke Rubutawa, Ba Wai Sharri Muke Musu Ba – Amina Ma’aji
- Usman Baba Pategi (1942 -2023): Rayuwa Da Shahararsa A Fagen Wasan Kwaikwayo
Kotun ta ce, matsayinsa a PDP ya sabawa sashe na 285(2) na kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Talla
Kwamitin ya umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta janye takardar shaidar cin zabe da ta baiwa Muftwang tare da ba Goswe sabuwar takardar shaidar cin zabe.
Talla