Hukumar ‘Yansanda ta fitar da sanarwa cewa mako guda ya rage kafin ta rufi shafin daukar sababbin ‘Yansanda a fadin Nijeriya.
Yanzu haka shafin ya samu masu neman aiki su kimanin mutum dubu dari biyar da bakwai, da dari bakwai da saba’in da hudu (547,774) a matsayin masu neman aiki Dan sanda a rundunar ‘yan sandan Nijeriya gabanin rufe shafin a ranar Lahadi mai zuwa, 26 ga Nuwamba, 2023 wanda zai cika makonni 6 na na wa’adin da hukumar ta sanya.
- Yadda ‘Yansanda Suka Min Duka Kamar Dan Ta’adda – Shugaban NLC
- A Sake Fasalin Rundunar ‘Yansandan Nijeriya
An buɗe shafin a ranar 15 ga Oktoba, 2023, makonni biyar da suka gabata.
Daga cikin 547,774 masu neman aiki, 358,900 sun yi nasara kuma sun cancanci zuwa zagaye na gaba na tsarin daukar ma’aikata wanda ya hada da yanayin kirar jikinsu da lafiyarsu da ingancin takaddunsu bayanansu.
An yi cire mutane akalla sama da 84,606 na masu neman aikin wadanda shekarunsu na haihuwa suke tsakanin shekaru 18 zuwa 25, inda aka fitar da su.
Jihar Kaduna ce Jiha ta farko a matsayin jihar da ta fi kowacce yawan masu nema aikin da mutum 40,272 sai Jhar Anambra wadda take a matsayin Jihana karshe da mutum 1664.
Kazalika Jihar Adamawa ce ta biyu da mutum 36,398, sai Jihar Borno da ta zo ta uku da mutum 32,048.
Jihar Benue na da 31,122 wadda ita ce a matsayin ta hudu, sai Jihar Katsina a matsayi na biyar mai mutum 30,202, sai Jihar Bauchi mai mutum 30,604 a matsayin ta 6 yayin da Jihar Kano ke bite mata a matsayin Jiha ta 7 da mutum 30,004.
Sauran Jihohin sun hada da Jihar Ebonyi mai mutum 2132, sai Jihar Legas mai mutane 2324. Jihar Bayelsa na da 2651 yayin da Abia ke da 2796.
Sufeto Janar na ‘yan sanda mai ritaya, Dr. Solomon Arase, ya bayyana jin dadinsa da yawan adadin manema aikin da aka samu da suka nuna sha’awar neman aiki na ‘yan sandan Nijeriya.
Tsohon Sifeton ya ce, Hukumar za ta yi iya bakin kokarinta don ganin daukar ma’aikatan an yi bisa ka’idojin da aka ayyana tare da duba cancanta da kuma adalci a yayin gudanar da aikin kamar yadda sanarwar Kakakin rundunar na kasa, Ikechukwu Ani, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 19 ga Watan Nuwambar 2023 da muke ciki.