Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Dokta Abdullahi Ganduje ya yi alhinin rasuwar daraktan masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Aminu Surajo Bono.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Edwin Olofu, ya fitar a ranar Talata, Dokta Ganduje, ya ce ya kadu matuka bayan samu labarin rasuwar fitaccen Daraktan.
- Zan Biya Wa Aminu S. Bono Duk Bashin Da Ake Bin Sa – Aisha Humaira
- An Saki Fursunoni 4,000 Don Rage Cunkoso A Gidajen Yari A Nijeriya
Ganduje wanda ya ce rasuwar Darakta Aminu S. Bono ba kamaramin rashi ba ne ga masana’antar Kannywood, inda ya kara da cewa rasuwar daraktan ta bar babban gibi a masana’antar.
Shugaban jam’iyyar, ya kara da cewa Darakta Bono ya yi amfani da lokacinsa wajen bunkasa masana’antar Kannywood ta hanaya gudanar da tsaftacacciyar rayuwa.
Ganduje ya ce, “Na kadu matuka da samun labarin rasuwar Darakta Aminu Surajo Bono. Wannan ba rashi ba ne kawai ga masana’antar Kannywood ba. Babban rashi ne ga al’umma.
“Ina amfani da wannan dama don mika ta’aziyya ga iyalansa da ‘yan uwansa da masana’antar Kannywood baki daya. Ina rokon Allah Ya ba su juriyar wannan rashi.
“Tabbas rayuwar Darakta Bono a cikin fina-finansa da kuma zahiri abar yabawa ce.”
Shugaban jam’iyyar, ya ce yana rokon Allah (SWT) da ya bai wa iyalansa da masana’antar kannywood juriyar wannan baban rashi, sannan ya roki Allah (SWT) da ya gafarta wa mamacin.
Da yammacin ranar Litinin ne Daraktan ya rasu, bayan ya dawo daga wajen aiki.
Rasuwarsa ta girgiza masana’antar Kannywood, inda abokan sana’arsa suka shiga yi masa addu’a da samun dacewar Allah SWT.
Da safiyar ranar Talata aka yi jana’izarsa a unguwarsu da ke Dandago a birnin Kano, sannan aka birne shi a makabartar Dandolo da ke Goron Dutse.