Rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa ta tsaurara matakan tsaro a fadin jihar gabanin hukuncin da kotun daukaka kara za ta yanke kan zaben gwamnan jihar.
A satin da ya wuce ne kotun daukaka kara ta sanya ranar yanke hukunci kan karar da Gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC ya shigar yana kalubalantar hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar, wadda tun farko ta tsige shi daga mukaminsa tare da ayyana dan takarar jam’iyyar PDP, David Obungudo.
- Ganduje Ya Yi Alhinin Rasuwar Darakta Aminu S. Bono
- An Saki Fursunoni 4,000 Don Rage Cunkoso A Gidajen Yari A Nijeriya
Idan za a tuna, a hukuncin kotun ya bayyana jam’iyyar PDP a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Sai dai Gwamna Sule bai gamsu da hukuncin kotun ba, inda ya garzaya kotun daukaka kara.
Mukaddashin kwamishinan ‘yansandan jihar, Shettima Muhammad, ya shaida wa manema labarai a garin Lafiya cewa rundunar ta baza jami’anta don hana tashin hankali.
Don haka ya gargadi jam’iyyun siyasa da magoya bayansu kan duk wani abu da zai haifar da tashin hankali a jihar.
“Ana kira ga shugabannin jam’iyyun siyasa da su ja hankalin magoya bayansu kan abin da zai haddasa tarzoma.
“Duk wani ko kungiyar da ta yi kokarin kawo cikas ga zaman lafiya, za su fuskanci fushin doka,” in ji shi.
Kwamishinan ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu kamar yadda suka saba, yayin da jami’an tsaro za su yi aikinsu.