Majalisar wakilai ta amince da kudirin gwamnatin tarayya na kashe naira tiriliyan 26 a tsakanin 2024 zuwa 2026.
Daga cikin wannan adadin da aka amince da shi, Naira tiriliyan 10.2 na yau da gobe ne daga cikin kudin da gwamnatin ke samu (ba bashi); Ma’aikatu (MDAs) za su lakume Naira Tiriliyan 4.49; bukata ta musamman da ka iya bijirowa, an ware mata Naira biliyan 200; an kuma tanadi Naira Tiriliyan 5.9 domin manyan ayyuka tare da wata bukata ta musamman akan Naira biliyan 7.
- NNPP Ta Yi Maraba Da Kiran Atiku Na Dunkulewar Jam’iyyun Adawa Don Kauda APC
- Zaben Nasarawa: ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaro Gabanin Hukuncin Kotun Daukaka Kara
Majalisar ta kuma amince da bukatar samar da karajin haraji na Naira tiriliyan 16.9; Cike gibin da aka samu a Kasafin kudi na Naira Tiriliyan 9, ta kuma amince a amso Naira Tiriliyan 7.8 a sabon rance (ciki har da karbar rance daga kasashen waje da cikin gida).
Wannan amincewar ta biyo bayan la’akari da karbar shawarwarin da rahoton Tsarin Kudi na Matsakaici na 2024-2026 (MTEF) da Takarda Dabarun tsimi da tanadi (FSP) na zauren majalisar ya bayar a ranar Talata.
Hon James Faleke (APC, Legas) ne ya gabatar da rahoton ga kwamitocin kudi, tsare-tsare na kasa da bunkasa tattalin arziki da bada tallafi, lamuni da kula da basussuka kuma kwamitin samar da kayayyaki wanda kakakin majalisar Abbas Tajudeen ya yi duba acikin rahoton a matsayin shugaba kuma ya amince da shi a zaman majalisar.