Firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci kuma ya gabatar da jawabi a taron shugabannin G20 da aka gudanar ta kafar bidiyo a ranar Laraba a nan birnin Beijing.
Li ya yi kira ga mambobin G20 da su ba da fifiko kan hadin gwiwar raya kasa da kuma adawa da siyasantar da batutuwan ci gaba.
- Xi Jinping Ya Gana Da Takwaransa Na Uruguay
- BRICS Ta Bi Sahun Sassan Dake Neman Kawo Karshen Rikicin Isra’ila Da Palasdinu
Li ya kara da cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen sa kaimi ga bude kofa ga kasashen duniya, da ba da damammakin samun ci gaba tare ga duniya, Li ya ci gaba da cewa, Sin za ta ci gaba da yin aiki tare da dukkan bangarori kuma a bayyane don ba da babbar gudummawa ga farfado da tattalin arziki, da ci gaban duniya da wadata.
Shugabannin kasashen mambobin G20, da shugabannin kasashe baki, da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa sun halarci taron. (Mai fassara: Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp