Rahotannin da aka gabatar sun nuna cewa, a halin yanzu, adadin hatsin da aka adana bisa sabbin fasahohin zamani a fadin kasar Sin ya riga ya kai tan miliyan 200, wato aikin adana hatsi a kasar ya shiga sabon mataki na adana hatsi ba tare da gurbata muhalli ba.
Alkaluman da hukumar adana kayayyaki da hatsi ta kasar Sin ta samar sun nuna cewa, tun daga shekarar 2021, kasar Sin ta fara daukar matakan adana hatsi ba tare da gurbata muhalli ba, ta hanyar yin amfani da sabbin fasahohin zamani, domin kyautata ingancin hatsi da tsimin hatsi da kuma rage hasarar hatsin.
Shugaban sashen adana hatsi da kimiyya da fasaha na hukumar adana kayayyaki da hatsi ta kasar Zhou Guanhua ya bayyana cewa, yanzu ana amfani da fasahohin zamani yayin da ake adana hatsi, wato ana adana hatsi a wuri mai sanyi domin tabbatar da ingancinsu. (Mai fassara: Jamila)