A wani hari da rundunar sojin saman Nijeriya ta kai a jiragen yakinta a ranar 24 ga watan Nuwamba, 2023, sun kai hare-hare ta sama kan tarin ‘yan ta’adda a wani kebabben wuri da ke tsakiyar bishiyoyi da yawa a cikin tsaunin Mandara.
A cewar mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet ya ce, ana iya ganewa daga faifan bidiyon harin cewa, ‘yan ta’addan na taruwa a wurin domin tattaunawa ko kuma suna shirin kai wani babban hari.
- Za Mu Samar Da Wutar Lantarki MW60 Ko Sola MW50 A Kowace Jiha -Gwamnonin Arewa Maso-Gabas
- Uba Sani Ya Baiwa Wadanda Suka Lashe Musabakar Karatun Alkur’ani Kujerun Hajji
“Sama da ‘yan ta’adda 100 dauke da muggan makamai aka gani suna tafiya cikin daji tare da wasu manyan motoci hudu. Sakamakon harin da aka kai ta sama ya nuna cewa an tarwatsa ‘yan ta’addan tare da lalata motocin dakon kayan.
“Bugu da kari, ana kyautata zaton cewa, kwamandoji a kungiyar Boko Haram, Abu Asad da Ali Ngulde, da kuma sauran ‘yan ta’adda irin su Ibrahim Nakeeb, Mujaheed Dimtu, Mustafa Munzir da mayaka da dama, na daga cikin ‘yan ta’addan da aka tarwatsa sakamakon hare-haren ta sama.”
Gabkwet ya ce, babban hafsan hafsoshin sojin sama, Air Marshal Hasan Abubakar, ya yabawa kwamandan rundunar sojin sama da jami’ansa, inda ya bukace su da su ci gaba da kyautata alaka da takwarorinsu na kasa domin ci gaba da kawar da ‘yan ta’addan.