Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon shugaban ma’aikatan gwamnati.
Nadin ya biyo bayan murabus din da tsohon shugaban ma’aikata, Alhaji Usman Bala ya yi na kashin kansa wanda ya kasance shugaban hukumar tun a gwamnatin baya kuma sabuwar gwamnatin ta ci gaba da aiki da shi.
- DA DUMI-DUMI: Gobara Ta Tashi A Babbar Kasuwar Kabba Ta Jihar Kogi
- Sojoji Da ‘Yan banga Sun Ceto Mutum 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi
Abdullahi Musa ya rike mukamin babban sakatare na gidan gwamnatin Kano, daraktan harkokin hukumomi, shugaba mai kula da ma’aikata a Ma’aikatar Ayyuka na Musamman, sannan kuma ya rike matsayin Darakta a ofishin Servicom.
Ya kammala digirinsa na farko a fannin dangantakar kasa da kasa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya samu digirinsa na biyu a fannin jagorancin al’umma da gudanar da mulki a Jami’ar Bayero ta Kano da kuma wani digiri na biyu a fannin dabarun tsaro da harkokin tsaro daga makarantar Sojoji ta Nijeriya, NDA Kaduna.
Gwamna Abba Kabir ya bukaci sabon shugaban ma’aikatan jihar da ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa ta hanyar bin duk dokokin da gwamnati ta tanada.