Jimillar ribar manyan masana’antun kasar Sin ta karu a karo na 3 a jere a watan Oktoba, inda ribar manyan masana’antu masu jarin a kalla yuan miliyan 20, kimanin dalar Amurka miliyan 2.81 ta karu da kaso 2.7 bisa dari a shekara, kamar dai yadda alkaluman da hukumar kididdigar kasar NBS ta fitar a Litinin din nan suka tabbatar.
Sashen masana’antun samar da kayayyakin sarrafawa ne ke kan gaba wajen zaburar da karin ribar masana’antun, sashen da ya samar da karuwar kaso 22.9 bisa dari na ribar, a gabar da fannonin dake bukatar kayayyakin sarrafawar ke kara farfadowa, wanda hakan ya ingiza karuwar farashi. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp